Hukumar zabe ta kara yiwa wasu sabbin jam'iyyu 5 rajista a Najeriya

Hukumar zabe ta kara yiwa wasu sabbin jam'iyyu 5 rajista a Najeriya

- Hukumar zabe ta INEC ta kara yiwa wasu sabbin jam'iyyu 5 rajista a nan kasar

- Shugaban hukumar zaben ya jaddada wa sabbin jam'iyyun cewa hukumar zata basu hakkokinsu kamar sauran jam'iyyun siyasa

- INEC ta gabatar da takardar shaidar rajista ga sababbin jam'iyyun

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta gabatar da takardar shaidar rajista ga wasu sababbin jam'iyyun siyasa guda 5 a kasar nan.

Sabbin jam'iyyun sune Action Democratic Party (ADP), All Democratic People’s Movement (ADPM), Advanced People’s Democratic Alliance (APDA), New Generation Party of Nigeria (NGP) da kuma Young Progressive Party (YPP).

KU KARANTA: 'Masu fasa-kwaurin kaya zuwa Najeriya zasu shiga halin tsaka mai wuya' - Comptroller Amajam

Hukumar zabe ta kara yiwa wasu sabbin jam'iyyu 5 rajista a Najeriya

Shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu a lokacin da yake gabatar da takardar shaidar rajista ga sababbin jam'iyyu 5

NAIJ.com ta ruwaito cewa shugaban hukumar zaben, Mahmood Yakubu, ya tabbatarwa sabbin jam'iyyun cewa hukumar zabe ta INEC zata basu hakkokinsu kamar sauran jam'iyyun siyasa dake kasar nan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu jami'an hukumar zabe INEC a gaban kotu kan cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel