Martani ga ministan matasa da wasanni solomon dalung

Martani ga ministan matasa da wasanni solomon dalung

- Wani dan Najeriya ya mayar da martani ga ministan matasa da wasanni kan kalaman da ya furta kan talakawan Najeriya

- Mutumin ya jaddada cewa talakawan Najeriya suka zabe gwamnatin nan har ya kai ga samun minista

- Mai magana ya ya ce talakawa sune gatan gwamnatin shugaba Buhari kuma ya gargadi ministan ya san irin kalaman da zai ke furtawa akansu

Naci karo da wata maganar da kayi cewar "Talakawa ne ke haddasa matsaloli a kasar nan". Idan har hakan ta tabbata to bazan yi mamakin jin haka daga bakinka ba saboda nasan cewar yanzu likafarka ta ci gaba tunda kayi adabo da talakawar da kake janyowa a jikinka lokacin yakin neman zabe.

Kafun akai ga samuwar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari wacce cikin ikon Allah talakawan da kake aibantawa da cewar sune matsalar kasa suka taru suka kafata har ka samu ofishin da yanzu haka kake tada komada, baka da wani batu a wancan lokaci wanda ya wuce batun inganta rayuwar talaka. Amma yanzu kuma da yake ka samu abin duniya sai talaka ya zamto matsala gareka.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, mai rubutun ya ce babu shakka duk mai hankali da hangen abunda ke kai komo a kasar nan yasan cewar talakawan da kake aibantawa ko yanzu sun maka rana tunda sun zabi gwamnatin Shugaba Buhari kuma gwamnatin ta yi maka suturar da baka taba samun irinta ba a rayuwar ka.

Martani ga ministan matasa da wasanni solomon dalung

Ministan matasa da wasanni solomon dalung

Mu talakawa muna da yakinin cewar shugaba Buhari yana iya bakin kokarin shi akan inganta walwalar mu, shi yasa ma hankalin shi bai konta ba bare yayi naman wuya irin wacce take wuyar ka.

KU KARANTA: Buhari ya ce lallai jami’an gwamnati su gana da Osinbajo

Duk wanda yasan minista kafun kafuwar gwamnatin shugaba Buhari kuma yasan minista a yanzu tabbas yasan cewar talakawa sunyiwa minista rana domin kuwa gwamnatin da suka kafa ta wanke minista ya fito tsatsaf a idon duniya. A lokacin da damuwar talakawa suke sa shugaba ramewa su minista kuwa sai cika suke kamar zasu fashe.

Inaso ministan yasan cewar talakawa sune gatan gwamnatin shugaba Buhari kuma yasan irin kalaman da zai ke furtawa akansu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ra'ayoyin 'yan Najeriya kan komawar shugaba Buhari Landan don duba lafiyarsa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel