Lai Mohammed ya ce babu rana da aka ajiye na dawowar Buhari

Lai Mohammed ya ce babu rana da aka ajiye na dawowar Buhari

- Lai Mohammed ya ce ba zai iya fadin cewa ga lokacin da Buhari zai dawo kasar ba

- Jawabin ministan na zuwa ne ‘yan kwanaki kadan bayan ana ta jita-jitan cewa Buhari zai dawo a farkon mako ko mako na biyu ga watan Yuni

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar kasar tun ranar 7 ga watan Mayu lokacin da ya koma birnin Landan don duba lafiyarsa

‘Yan kwanaki bayan rahoton da Sahara Reporters ta yin a cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo Najeriya tsakanin farkon mako da na biyu ga watan Yuni, ministan bayanai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa babu wani rana da aka ajiye na dawowar shugaban kasar.

Mohammed ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni, lokacin da ya fito a wani shiri da akeyi a gidan talbijin din Channels Television mai suna Politics Today.

A cewar sa, shugaban kasa Buhari ya bayyana kafin ya tafi, cewa likita ne zasu iya fadin ranar dawowar sa.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya ce lallai jami’an gwamnati su gana da Osinbajo

Da yake amsa tambaya a kan lokacin da Buhari zai dawo kasar, Mohammed ya ce: “Ina ganin shugaban kasar ya fayyace komai kafin tafiyar sa cewa likita ne zai fadi ranar dawowarsa. Labari abun dogaro a yanzu shine daga uwargidan shugaban kasar ta bayyana cewa shugaban kasar na samun lafiya sosai. Shine abun da zamu iya fadi zuwa yanzu.”

Kan cewa ko ya yi magana da shugaban kasar tunda ya tafi ministan y ace: “A’a ba lallai sai nayi ba.

Kan ko uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta ga maigidanta a lokacin da ta je Landan, Mohhammed ya ce: “Babu wani dalilin da zai sa ni yin kokwanto a kan matar shugaban kasar. Idan har uwargidan shugaban kasar zata fito ta ce ‘na ga mijina kuma yana nan lafiya’, babu wani dalili da zai san a ji shakkun ta.”

Shugaban kasa Buhari ya tafi Landan ne don ganin likita a ranar Lahadi 7 ga watan Mayu jim kadan bayan ya tarbi ‘yan matan Chibok 82 da aka saki.

Kafin tafiyar sa, ba kasafai ake ganin shugaban kasar a cikin jama’a ba, wannan ya rura wutan jita-jita a kan lafiyar sa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku ra'ayin yan Najeriya a kan dawowar shugaba Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel