Buhari ya ce lallai jami’an gwamnati su gana da Osinbajo

Buhari ya ce lallai jami’an gwamnati su gana da Osinbajo

- An rahoto cewa shugaban kasa Buhari ya yi burus da ganawa ministoci da mataimakansa da sukayi kokarin ganinsa a Landan

- Wasu daga cikin su sun so ya sanya masu hannu a kan wasu takardu amma ya yi watsi da su

- Shugaban kasar ya ce lallai tunda Osinbajo na a matsayin mukaddashin shugaban kasa ne shine keda ikon yin haka

An rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci wasu mataimakansa da ministoci da ke neman yardar sa a kan wasu takardu, da su hadu da mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Shugaban kasar wanda ke hutun ganin likita a Landan ya mika mulki ga Osinbajo kafin ya bar kasar kuma tun lokacin yana bin abubuwa yadda ya kamata.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa wasu jami’an gwamnati sun yi tattaki zuwa Landan don samun yardarm shugaban kasa amma ya zuba masu kasa a ido inda ya ce lallai a mika dukkan takardu ga Osinbajo don yarda da sa hannu.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa sarkin Kano ya kaiwa mukaddashin shugaban kasa Osinbajo ziyara

Wata babban majiya na gwamnati ta ce: “Duk da cewan yana samun sauki sosai, shugaban kasar na iya bakin c=kokarin sa don ganin an tsayar da fadar shugaban kasa guda daya.

“Ya ki ganin wasu manyan jami’ai da sukayi tattaki zuwa Landan don ganinsa a maimakon kasancewa a bakin aikinsu. Ya kuma dawo da fayil da takardun wadanda suka kai Landan.

“Shugaban kasar ya ba da umurnin cewa akai dukkanin wasu fayil, takardu da al’amuran dake bukatar hukunci ga mukaddashin shugabna kasa. Baya son a raba kan gwamnati. Buhari na nan aka tsatsauran ra’ayin sa."

Game da rade-radin cewa ba’a bari Aisha Buhari ta ga shugaban kaar ba a lokacin da ta je Landan, majiyar ta ce ba gaskiya bane, ta ce lallai uwargidan shugaban kasar ta gana da shi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Kalli bidiyon NAIJ.com TV kan ko yan Najeriya sun yi kewan shugaba Buhari:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel