'Gurguwar dabara ce kama samarin arewa da ke son korar Ibo'

'Gurguwar dabara ce kama samarin arewa da ke son korar Ibo'

- An shawarci gwamnati da kada ta ingiza wutar rikicin kabilanci

- Taron shugaba Osinbajo da shuwagabannin tsaro yayi nazarin yadda lamarin ka iya zama rikici

- An yanke shawarar ci gaba da zaunawa da shuwagabannin kabilu ba tare da kame su ba

A kiraye-kiraye da bangarorin 'yan aware na kasar nan ke yi a layi kabilanci da ma bangaranci, shuwagabanni tsaro sun dukufa kan ganin yadda zasu shawo kan lamarin kafin ya zama wani babban kalu-balen tsaro.

A tarukan da suka yi na baya bayan nan, an gano cewa, kama wadanda ke rura wutar daga arewa ko kudu yana dada kambama rikicin, musamman ganin cewa 'yan siyasa har suna mara wa samarin baya daga kowanne bangare.

KU KARANTA KUMA: Ku haqura kuso Najeriya, ake shawartar kabilar ibo

'Gurguwar dabara ce kama samarin arewa da ke son korar Ibo'

'Gurguwar dabara ce kama samarin arewa da ke son korar Ibo'

A arewa, an sami wasu dattijai na mara wa samarin yankin baya kan barazanar su ta korar kabilun kudu, a kudu kuma, hukumomi sun kula da yadda ake tururuwa zuwa gidan dan takife Nnamdi Kanu, ciki kuwa harda sanatoci.

Karshe dai an sami matsaya kan cewa dole a kyale su su ci karensu ba babbaka ba tare da an kama su ba, an kuma duba da cewa wanda duk ya wuce gona da iri zai fuskanci fushin hukuma, sannan zama da dattijan bangarorin biyu zai bada gwarin gwiwar shawo kan lamarin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel