An sake kama wata bisa zargin garkuwa da mutane

An sake kama wata bisa zargin garkuwa da mutane

- Kiris ya rage a kashe ta a titi

- Ana zargin ta da satar mutane

- An mika ta ga hukuma

A Ikorodu dake jihar Legas, an sami wata mata da samari suka kama bisa zargin cewa wai tana hada kai da barayi don sata da garkuwa da mutane don daukar fansa. An same ta tuni samari sun lakada mata duka suna kokrin kashe ta bisa wannan zargi, amma daga baya an sami wasu sun cece ta sun kuma mika ta ga hukumar yansanda.

Ba a dai fadi sunan ita wannan mata ba, ba'a kuma sami wani takamaiman bayani daga hukuma ba ya zuwa yanzu.

KU KARANTA KUMA: Ku haqura kuso Najeriya, ake shawartar kabilar ibo

A baya bayan nan dai ana kara samun karuwar sata da fashi da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, wadda an kasa shawo kanta kacokan, duk da sa'ar kame wasu da hukuma keyi jefi-jefi.

Ana zargin yawan karuwar talauci dai na daga cikin abu da ya jawo karuwar kananan laifuka, kamar zata da fashi, saboda da yawa masu kudi ake hari domin kwatar kudinsu, kuma in an sami kudin a sake su a kame wasu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel