Ku haqura kuso Najeriya, ake shawartar kabilar ibo

Ku haqura kuso Najeriya, ake shawartar kabilar ibo

- Muhawara na kara zafafa tsakanin kudu da arewar Najeriya

- An ci gaba da hararar juna tsakanin kabilun kudu da arewa

- Anyi kira da kowa ya so juna tsakanin makwabta kabilu

Cif Hope Uzodinma, sanata daga jihar Imo, a majalisar dattijai, na kabilar Ibo, ya baiwa kabilun kudu maso gabashin Najeriya shawara da su hakura su zauna a ajeriya, su girmama doka, su kuma bada irin tasu gudummawar don ci gaban kasa.

Ya yi wannan kiran ne a birnin landan na Ingila, inda a bagare daya kuma ya kira ga gwamnatin tarayya da ta ciyar da yankin na gabashin najeriya gaba, inda yayi kira da a taimaka wa yankin nasa a kafa musu wata babbar cibiya ta kere-kere wadda zata tafiyar da tattalin arzikin yankin, musamman ganin dama kabilar sun kware wajen kere-kere.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Jihar Kaduna ta hana hawa babur

Ku haqura kuso Najeriya, ake shawartar kabilar ibo

Ku haqura kuso Najeriya, ake shawartar kabilar ibo

Sanatan na tsokaci ne a laccar da ya bayar kan ci gaban kabilar ibo a duniya, inda ya yi kira ga kabilar da su hakura da batun ballewa daga Najeriya, harma kuma ya buga misali da yan siyasar kabilar da suka yi fice a duniya da wasu kasashen dama iyaye dattijai da suka kafa kasar najeriya.

Karshen taron ya watse dai da alwashin da masu halartar taron sukayi, na sake nuna soyayyar su ga hadin kan Najeriya, da kuma kira ga sanatan da ya nemi wata kujerar a zabuka masu zuwa, kujera wadda ta fi tasa a yanzu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel