Tsohon shugaba Jonathan yayi magana kan mulkin Buhari

Tsohon shugaba Jonathan yayi magana kan mulkin Buhari

- An dade ba'a ji duriyar tsohon shugaban Najeriya Jonathan ba

- Jonathan yace matsalolin najeriya sun fi karfin mutum daya

Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Dr. Goodluck Ebele Jonathan yayi ammana da cewa matsalolin Najeriya ba abu ne wanda mutum daya kan iya warwaresu ba.

Tsohon Shugaban ya cigaba cewa musayan maganganu da zargi da mutanen bangarorin. Najeriya ke jefa wa juna ba zai kai kasar ga tudun na tsira ba. Sai dai, kamata yayi duk a hada karfi da karfe waje daya domin gina kasar.

Tsohon Shuga Jonathan din ya bada wannan shawarar ne ta bakin tsohon sakatare na gwamnatin tarayya Sanata Ayim Pius Ayim a wajen lecture na 5 don tunawa da marigayi Farfesa Celestine O. E Onwuliri.

Tsohon shugaba Jonathan yayi magana kan mulkin Buhari

Tsohon shugaba Jonathan yayi magana kan mulkin Buhari

Farfesa Celestine Onwuliri yana daga cikin jama'an da suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon hadarin jirgin sama kirar Mc Donnell Douglas 83-MD da ya faru a ranar 3 ga watan yuli na shekarar 2012 a garin Legas.

"Mutane sunyi maganganu da yawa akan matsalolin Najeriya amma ni abin da zan iya cewa shine matsalolin sunfi karfin mutum daya" Inji Jonathan.

A cikin bayanin da yayi, tsohon gwanan Jihar Imo Chief Ikedi Ohakim yayi juyayin rashin Farfesa Celestine Onwuliri da ma wasu 'yan Najeriya. Kuma ya kara da cewa matukin jirgin ma bai da shedar tatancewa na tukin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi shugaba Buhari da kula da shanun sa fiye da al'ummar Najeriya

An zargi shugaba Buhari da kula da shanun sa fiye da al'ummar Najeriya

An zargi shugaba Buhari da kula da shanun sa fiye da al'ummar Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel