Hukumar yan sanda sun yi ram kananan yara masu fashi da makami a jihar Benue

Hukumar yan sanda sun yi ram kananan yara masu fashi da makami a jihar Benue

Jami’an yan sanda a jihar Benue sun damke matasa yan kasa da shekara 20 guda 3 wadanda suka kware wajen fasa gidajen jama’a a garin Makurdi, babban birnin jihar Ribas.

An bayyanasu ne jiya a hedkwatan huumar yan sandan jihar inda kwamishanan yan sandan, Bashir Makama yace an damke su ne a unguwan Wadatan garin Makurdi.

Yace:” Gungun yan fashin ya kunshi Aondokura Terngu,dan shekar 15, Denen Tyonenge, 14, Tersoo Jigba,14, da Emmanuel Onaji, 16.

Hukumar yan sanda sun yi ram kananan yara masu fashi da makami a jihar Benue

Hukumar yan sanda sun yi ram kananan yara masu fashi da makami a jihar Benue

“Yaran sun bayyana cewa lallai sune wadanda ke fasa gidajen jama’a da tsakar rana kuma su dibe kayayyaki yayinda masu gida basu nan."

KU KARANTA: Ya kashe dan achaba kan naira 100

“A yayin harin kuma muka dame wani mutum a kauyen Pika Mbasur a Gboko wanda ke ikirarin cewa shi soja ne. Bayan bincike an samu wasu kayayyakin soja a wurinsa wanda ya kunshi takalmin soja, kayan soja da sauran su.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Cif Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Cif Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel