Matar babban mai garkuwa da mutane ‘Evans’ tana neman afuwan gwamnati

Matar babban mai garkuwa da mutane ‘Evans’ tana neman afuwan gwamnati

Uwargidan babban biloniyan mai garkuwa da mutane, Chikwudubem Onwuamadike, a.k.a Evans, tace tana zargin kishiyar mahaifiyan mijinta da yi masa asiri tun yana shekara 4 da haihuwa.

Yar shekara 31 tayi wannan bayani ne yayinda tayi hira da jarida Vanguard inda tayi Magana akan damke mijinta da hukumar yan sandan Legas tayi.

Tana miko kokon rokonta ga gwamnatin tarayya su taimaka su saki mijinta kana kuma wadanda ya taba yin garkuwa da mutanensu suyi masa afuwa.

Matar babban mai garkuwa da mutane ‘Evans’ tana neman afuwan gwamnati

Matar babban mai garkuwa da mutane ‘Evans’ tana neman afuwan gwamnati

Tace: “ Ina zargin kishiyar mahaifiyarsa da yi masa asiri. Ban san abinda tayi masa yana karami ba amma ya fada mana.

“Ina rokon gwamnati ta yafe masa, a yanzu da nike Magana ina tsugunne da yarana muna kukan neman gafara. Kuji tausayinmu. Bai san abinda yakeyi ba. Na shirya dawowa Najeriya domin rook. Abinda nike karantawa a labarai na da ban tsoro.

“Duk da cewan ban samu labarin ya kasha kowa ba amma duk wadanda ya jima rauni da kuma ya dauki kudadensu su yafe masa saboda ni da yarana. Su yafe masa zai tuba ga ubangijinsa.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel