Yadda mukayi fashi da makami muka sace N200m – Evans

Yadda mukayi fashi da makami muka sace N200m – Evans

Wani babban mai garkuwa da mutane, Chukwudi Onuamadike, wanda akafi sani da Evans ya bayyana yadda shi da abokan aikinsa suka fr ma motocin kudi kafin dubunshi ya cika.

Yayinda yake Magana da manema labarai ranan Juma’a, Evans ya bayyana cewa a daya daga cikin hare-haren da suka kai titin Aba-Port Harcourt a jihar Abiya, sun sace N200m.

Game da cewarsa, “ A shekarar 2007, nayi tafiya zuwa kasar afrika ta kudu domin safarar muggan kwayoyi sannan na dawo Legas bayan wani wanda yaki biyana kudin kwayar ya harba ni a kafada.

Kasugumin mai garkuwa da mutane : Yadda mukayi fashi da makami muka sace N200m – Evans

Kasugumin mai garkuwa da mutane : Yadda mukayi fashi da makami muka sace N200m – Evans

“Da dan kankanin kudin da na dawo da shi Najeriya, wani abokina mai suna Kingsley ya gabatar da ni wata kungiya mai suna ‘ Too much money’ a jihar Abia.”

“Sai muka kwace wata mota da muka gani a titin Aba-Port Harcourt domin tare motar banki. da muka tare motar muka samu N80m kuma aka bani kaso na N1.8m”.

KU KARANTA: Osinbajo bai kama da dan Najeriya

Evans ya kara da cewa a wata hari da suka kai titin Umuahia inda suka sake tare wata mota suka kwace kudi kuma ya samu N7m wanda ya kara bunkasa kasuwancinsa da shi.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel