Osinbajo baya kama da yan Najeriya inji wani malamin jami'a

Osinbajo baya kama da yan Najeriya inji wani malamin jami'a

Wani malamin jami'a kuma shugaban tsangayar karatu na koyon aikin jaridar jami'ar jihar Delta Emmanuel Ufuophu-Biri yayi wani dogon rubutu inda ya bayyana yadda mukaddashin shugaba Buhari watau Yemi Osinbajo ya sa bamban da yan Najeriya.

Malamin jami'ar yayi dogon sharhin ne bayan a yadda yace ya kammala. Kallo tare da sauraron mataimakin shugaban kasar a gidan talabijin din jihar a wata ziyarar da ya kai a jiya.

Malamin jami'ar ya ci gaba da cewa yadda yaga Osinbajo yana sauraron jama'a sannan kuma yana basu amsa sannan yana mu'amalantar su kwata-kwata bai yi kama da yadda yan Najeriya ke yi ba idan sun samu mulki.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Malamin jami'ar ya ci gaba da cewa wadannan halayen nashi da ma wasu ya sa nike shakkun anya ko dan Najeriya ne?

Osinbajo baya kama da yan Najeriya inji wani malamin jami'a

Osinbajo baya kama da yan Najeriya inji wani malamin jami'a

A wani labarin kuma, A karo na biyu fadar shugaban Najeriya ta ce bata jin dadin yadda wasu ‘yan tsiraru ke son shiga tsakanin shugaba Mohammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Osinbajo, bisa ci gaban da ake samu a kasar.

Mai baiwa shugaban ‘kasa shawara kan harkokin siyasa Sanata Babafemi Ojudu, yace sun lura da cewa wasu ‘yan ‘gaza gani’ sun dage sai sun shiga tsakanin shugaban Buhari da mataimakinsa, bayan kuwa shugaban da mataimakinsa duk abu ‘daya ne.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel