Ban karya dokar kasa ba domin ina da 'yancin fadin ra'ayi na - Farfesa Ango Abdullahi

Ban karya dokar kasa ba domin ina da 'yancin fadin ra'ayi na - Farfesa Ango Abdullahi

- Dattijon arewa Farfesa Ango Abdullahi ya sake mayar da martani kan batun korar kabilar ibo daga arewa

- Ana cigaba da cece-kuce tsakanin kabilun Najeriya

- Ango Abdullahi yace baiyi laifin komai ba

Farfesa Ango Abdullahi ya zanta da yan jarida inda ya ce bayyi wani laifi ba. A ganawarsa da manema labarai, Wadda ba'a karasa ba saboda ya hasala, farfesan yace dama can Najeriya kanta a rabe yake.

'Tun 1966 kasar Najeriya take a rabe al ummunta basu sake yarda ko daraja juna ba'. Ya sake cewa.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai dawo nan ba da jimawa ba – Gwamnan APC ya bayyanaShugaba Buhari zai dawo nan ba da jimawa ba – Gwamnan APC ya bayyana

Ban karya dokar kasa ba domin ina da 'yancin fadin ra'ayi na - Farfesa Ango Abdullahi

Ban karya dokar kasa ba domin ina da 'yancin fadin ra'ayi na - Farfesa Ango Abdullahi

Da aka tambaya shi ko zaman buya yake sai yace, 'in da buya nake zaka ganni? Ai banyi wani laifi ba, fadin albarkacin baki na nayi.

Farfesan ya jaddada cewa tarihi ya nuna arewa da kudu sun ci arzikin juna a lokutan mulkin mallaka. Ya kuma kara da cewa, shi yana bayan samari da suka baiwa kabilar ibo wa'adin ficewa, duk da sauran datawan arewa basu bi irin ra'ayin ba.

A karshe ya sake nanata cewa in dai mutanen kudu suna son su kafa kasarsu to ya kamata su tafi can gida su kafa, su bar arewa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel