Dalilai 6 da ke hana mutane taimakawa da jininsu a asibitocin Najeriya

Dalilai 6 da ke hana mutane taimakawa da jininsu a asibitocin Najeriya

- Faith Ajani, babban likita ne kuma jami’i a kungiyar ‘Blood Drive Initiative’ ya yi kira ga mutanen Najeriya da su yawaita bada gudunmawar jini domin ceto rayukar mutanen dake bukata.

Ajani ya fadi haka ne ranar Laraba a wajen taron tunawa da ranar bada gudunmawar jini da ake yi kowace shekara Abuja wanda ke da taken ‘’Me za/ki iya yi? Taimaka da jini. Bada jini yanzu. Bada jini lokaci lokaci’’.

Likitan ya koka da yadda mafi yawan asibitocin Najeriya ke fama da karancin jini a ma’ajiyar jinin su wanda kafin a sami jinni a lokutta da dama sai an biya ko kuma dan uwan mara lafiyar na bukata sai a fita nema hurjanjan.

NAIJ.com ta samu labarin cewa ya ce hakan na faruwa ne saboda rashin sanin muhimmancin bada jini, da jiyeshi har zuwa lokacin da za a bukata.

Ya ce babbar dalilan da ke hana mutanen Najeriya bada jini sun hada da

1 – Rashin sanin muhimmancin bada jini, da jiyeshi har zuwa lokacin da za a bukata.

2 – Zato da masu bada jini keyi na siyar wa matsafa Jininsu.

3 – Mutumin da ya fito musamman daga yankin Arewa ba su yardasu bada jininsu hakan kawai ba wai don kila a bukata nan gabasaboda yarda da suke dashi cewa ciwo jarabawace daga Allah abari har sai bukatar hakan ya taso tukuna sai a nemi yin haka.

Dalilai 6 da ke hana mutane taimakawa da jininsu a asibitocin Najeriya

Dalilai 6 da ke hana mutane taimakawa da jininsu a asibitocin Najeriya

4 – Mutumin da ya fito musamman daga yankin gabacin kasar bai damu da ko ya bada jini ba ko a a shidai yaji ammai a aljihunsa kawai. Ko ya akeso ma zai yi.

5 – Mutumin da ya fito musamman daga kudancin kasar kuwa ya danganta bada jini da addininsa domin wasu cikin su sunce addininsu ya haramta musu bada jininsu kad’an.

6 – Rashin wayar wa mutanen karkara da kai akan muhimmancin taimakawa marasa lafiya da jini.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu, Inji Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel