Gamayyar kungiyoyin Inyamurai sun fitar da sunayen wadanda za su yi takarar shugaban kasa a 2019

Gamayyar kungiyoyin Inyamurai sun fitar da sunayen wadanda za su yi takarar shugaban kasa a 2019

Gamayyar kungiyoyi uku na inyamurai da suka hada da ‘The World Igbo Youth Congress (WIYC)’, ‘The Igbo Students’ Association (ISA)’, da ‘The South-East Women Professionals (SWP) sun fitar da jerin sunayen wadanda suke so su tsaya takaran shugabancin kasar nan a zaben 2019.

Kungiyoyin dai sun yanke wannan hukunci ne bayan wani babban taro da suka gudanar a garin Enugu a jiya Juma’a.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kungiyar Ohaneze Youth Council OYC ta bukaci a samu shugaban kasa Inyamuri shekarar 2019 ko kuma ta tabbatar da samar da Biafra a shekarar 2020.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Mutanen da suka zaba sun hada mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu, Tsohon gwamnan Anambra Peter Obi, gwamnan jahar Imo, Rochas Okorocha, Tsohon gwamnan Abia, Orji Uzor Kalu, da uwargidan tsohon shugaban kasa Dame Patience Jonathan.

Gamayyar kungiyoyin Inyamurai sun fitar da sunayen wadanda za su yi takarar shugaban kasa a 2019

Gamayyar kungiyoyin Inyamurai sun fitar da sunayen wadanda za su yi takarar shugaban kasa a 2019

Sauran sun hada da Air Comodore Ebitu Ukiwe, (rtd.), Lt. Gen. Azubuike Ihejirika (rtd.), Oby Ezekwesili, Prof. Pat Utomi, Prof. Onyebuchi Chukwu, Senator Anyim Pius Anyim, Senator Hope Uzodinma, da sauransu.

Kungiyar ta ce za ta tantance wadannan mutane domin ta fitar da mutum daya da zai yi takarar shugaban kasar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel