Jam'iyyar APC ta karyata rahoton cewa wai ta kori dan Majalisa Hon. Jibrin

Jam'iyyar APC ta karyata rahoton cewa wai ta kori dan Majalisa Hon. Jibrin

- An dakatar da Hon. jibril daga majalisa kan batun kale da rashin ladabi

- Batun wai an kori Abdulmimini Jibrin daga jam'iyyar APC ya tada kura

- Jam'iyyar APC ta mayar da martani

A makon da ya gabata, an sami rahotanni dake yawo kan cewa an dakatar da Hon. Abdulmumini Jibril daga majalisar wakilai, bayan da aka dakatar dashi daga majalisar watan shekaranjiya, bayan da aka zarge shi da rashin ladabi ga majalisa, kab batun kasafin kudi na bara.

Jam'iyyar reshen Kano, ta fitar da sanarwa ta bakin Bashir Y. Karaye, ta karyata batun korar tasa.Inda yace zaqe wa ce ta wani dan jam'iyya kawai.

"Mun sami labarin wai an kori Hon. Jibrin daga jam'iyyar mu, amma ba da yawunmu ba, Hon. Jibrin, mutum ne mai daraja ga jam/iyyarmu da ma Najeriya baki daya, kuma yana nan daram," inji sanarwar.

Jam'iyyar APC ta karyata rahoton cewa wai ta kori dan Majalisa Hon. Jibrin

Jam'iyyar APC ta karyata rahoton cewa wai ta kori dan Majalisa Hon. Jibrin

Ya cigaba da cewa wannan labari abin takaici ne domin Abdulmumin Jibrin yana daya daga cikin jigogin Jam'iyar APC a Jihar Kano da ma kasa baki daya. Wannan labarin da an ce ya fito ne daga wani jami'in jam'iyar da yayi amfani da matsayinsa a jam'iyar ta hanyar da bai dace ba.

Jam'iyyar tana amfani da wannan daman ta shaida ma jama'a cewa Shugaban Jam'iyar na Jiha wato mai girma gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, da shugaban zababun 'yan commitee na jihar duk basu da hannu ko masaniya akan lamarin.

Jam'iyar tana kira da jama'a da suyi watsi da maganar kuma zatayi bincike don tsamo duk masu hannu a cikin wannan aika-aikan don a hukunta su.

Jam'iyyar baza ta lamunci rashin da'a ba ko halin batanci musamman a wannan lokacin da take kokarin hada kan jama'a da kuma cika masu alkawuran da suka yi masu.

"Muna son mu tunatar da jama'a cewa Hon. Abdulmumin Jibrin ya taka rawar gani sosai a jam'iyar kuma baza manta da irin gudan mawar da ya bada ba wurin ginawa da raya jam'iyar. Muna amfani da wannan daman don yi masa godiya domin biyaya da hidima da yake ma jam'iyya."

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel