Sojojin Najeriya sun cafke wani dan Boko Haram dauke da makamai a Bauchi

Sojojin Najeriya sun cafke wani dan Boko Haram dauke da makamai a Bauchi

- Rundunar sojin Najeriya ta kama wani da ake zargin dan Boko Haram ne

- An kama shine dauke da bindigogin guda biyu

- Kamun na shi ya biyo bayan wani kakkaba da rundunar soji ta yi

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da kamun wani dan Boko Haram mai suna AliyuAhmed amma anfi sanin sa da Aliko dake boye a wani kauye a jihar Bauchi.

Kakakin rundunar soji Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ne ya tabbatar da kamun a wata sanarwa da aka saki a daren ranar Juma’a, 16 ga watan Yuni.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai dawo nan ba da jimawa ba – Gwamnan APC ya bayyanaShugaba Buhari zai dawo nan ba da jimawa ba – Gwamnan APC ya bayyana

Sojojin Najeriya sun cafke wani dan Boko Haram dauke da makamai a Bauchi

Dan ta'addan mai suna Aliyu Ahmed

A cewar sa rundunar sojin sun kama dan ta’addan ne dauke da makamai a wani zagaye da suke yi.

Sojojin Najeriya sun cafke wani dan Boko Haram dauke da makamai a Bauchi

Bindigogin da aka same shi da su

kwanan nan, NAIJ.com ta rahoto cewa rundunar sojin Najeriya dake gudanar da aiki a Potiskum sun kama wani gagarumin kwamandan Boko Haram a jihar Yobe.

An kama dan ta’addan mai shekaru 35, Abubakar Adamu wanda aka fi sani da ‘Pepper’ a yankin New Prison Potiskum, karamar hukumar Potiskum dake jihar Yobe.

NAIJ.com ta samu labarin cewa an kama Adamu ne a ranar Lahadi, 14 ga watan Mayu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com TV don ganin yadda rundunar sojin sama ke shirya ma yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf

Kungiya ta bukaci Buhari ya yiwa gwamnatocin bayan sa binciken kwa-kwaf
NAIJ.com
Mailfire view pixel