Shugaba Buhari zai dawo nan ba da jimawa ba – Gwamnan APC ya bayyana

Shugaba Buhari zai dawo nan ba da jimawa ba – Gwamnan APC ya bayyana

- Gwamna Bello ya jagoranci taron addu’o’I na musamman ga shugaban kasa Buhari a ranar Juma’a

- An gudanar da addu’an ne a lokacin sallar Juma’a a Lokoja babban birnin jihar Kogi

- Taron ya samu halartan manyan mutane kamar su tsohon gwamnan jihar Kano

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya ba yan Najeriya tabbacin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo kasar nan ba da dadewa ba daga hutun jinya da ya tafi birnin Landan.

Gwamna Bello ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a 16 ga watan Yuni lokacin da ya jagoranci manyan ‘yan Najeriya gurin addu’a don samun lafiyar shugaban kasar.

Gwamnan ya bayyana cewa shugaban kasa Buhari zai dawo nan kusa domin ya ci gaba da kyawawan ayyuka na gyara kasar.

Vanguard ta rahoto cewa an gudanar da addu’o’in ne a lokacin sallar Juma’a a masallacin gidan gwamnati a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin Najeriya sun kama masu safarar yara da yara a jihar Yobe

Daya daga cikin wadanda suka halarci taron shine tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Kabiru Gaya.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa gwamnatin jihar Sokoto ta kashe kimanin naira miliyan 91 don daukar nauyin malaman musulunci zuwa kasar Saudiya don yin aikin Umurah.

Da yake magana a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, kwamishinan kula da harkokin musulunci na jihar Sakkwato, Alhaji Mani Katami ya bukaci malaman da zasu tafi umuran da suyi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’an samun lafiya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com kan dawowar Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel