Igbo su yi wa kansu kiyamul laili - MASSOB

Igbo su yi wa kansu kiyamul laili - MASSOB

- Gamayyar kungiyoyin tsagerun Niger Delta mai arzikin man fetur a Najeriya, ta nemi 'yan arewacin kasar dake zaune a yankin su da kuma kamfanonin hakar man fetur dinsu su bar yankinsu

- Kungiyoyin sun ba 'yan arewa da ke zaune a yankin wa'adin watanni uku wato nan da ranar 1 ga watan Oktoba su fice daga yankin

- Sun kuma bukaci gwamnatin tarayyan Najeriya da ta mayar musu da duk rijiyoyin man fetur da 'yan arewacin kasar suka mallaka

Wata gamayyar kungiyoyin tsagerun Niger Delta mai arzikin man fetur a Najeriya, ta nemi 'yan arewacin kasar dake zaune a yankin su da kuma kamfanonin hakar man fetur dinsu su bar yankinsu.

Kungiyoyin sun ba 'yan arewa da ke zaune a yankin wa'adin watanni uku wato nan da ranar 1 ga watan Oktoba su fice daga yankin na su.

KU KARANTA KUMA: Labaran da ke rada cewa an kashe yan kabilar Igbo a Kaduna karya ne – El-Rufai

Igbo su yi wa kansu kiyamul laili - MASSOB

Igbo su yi wa kansu kiyamul laili inji kungiyar MASSOB

Haka zalika, sun bukaci gwamnatin tarayyan Najeriya da ta mayar musu da duk rijiyoyin man fetur da 'yan arewacin kasar suka mallaka a yankin .

Yayin da su kuma masu fafutukar kafa kasar Biyafara a yankin kudu maso gabashin kasar kuma suka umarci 'yan kabilar Igbo a kan lallai suyi ma kansu kiyamun laili su bar yankin arewa su koma yankinsu na kudu maso gabashin kasar don kafa ta sau kasar.

Matakin dai ya biyo bayan wani wa'adin wata uku da wasu kungiyoyin matasan arewa suka diba ma 'yan kabilar Igbo a kan su fice daga yankin arewaci.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Har yanzu Najeriya na da wani matsayi a Afrika ?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel