Majalisar Tarayya na da ikon yi wa kasafin kudi katsalandan - Dogara

Majalisar Tarayya na da ikon yi wa kasafin kudi katsalandan - Dogara

- Kakakin majalisa, Yakubu Dogara ya ce majalisar tarayya na da ikon yima kasafin kudi katsalandan

- Ya ce hakan na yiywuwa ne idan har majalisa ta ga akwai ayyuka da ya kamata a kara ko a cire

- Wannan martani ne ga furucin da mukaddashin shugaban kasa ya yi na cewa majalisa bata da ikon yiwa kasafin kudi katsalandan

Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya bayyana cewa Majalisar Tarayya na da ikon tsoma hannu cikin sha’anin kasafin kudi ta hanyar kara wasu ayyuka ko kuma cire wasu da ta ke ganin akwai bukatar yin hakan.

Dogara ya furta hakan ne a lokacin da ya ke maida martani ga wani kudiri da dan majalisa Lawal Abubakar daga Adamawa ya gabatar.

Abubakar, wanda dan APC ne, ya yi ikirarin cewa Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ne ya yi furucin sau biyu a wurare mabambanta.

KU KARANTA KUMA: Labaran da ke rada cewa an kashe yan kabilar Igbo a Kaduna karya ne – El-Rufai

Majalisar Tarayya na da ikon yi wa kasafin kudi katsalandan - Dogara

Majalisar Tarayya na da ikon yi wa kasafin kudi katsalandan inji Dogara

Ya ce da kunnen sa ya ji kuma ya karanta inda mukaddashin shugaban kasar ya ce Majalisar Tarayya ba ta ikon yi wa kasafinn kudi katsalandan kafin a amince da shi.

Dogara ya ce ai dokar kasa ta fayyace wa kowane bangare na gwamnati irin ayyukan da zai rika gudanarwa. Kuma wannan dokar ta bai wa majalisa ikon sa hannnun ta a sha’anin kasafin kudi domin ragewa, karawa ko kuma yin wasu gyare-gyare da suka kamata.

Ya kara da cewa wani ma abin lura shi ne, wannan doka ta bayyana cewa rashin aiwatar da tsare-tsaren kasafin kudi kan sa babban laifin yi wa doka karan-tsaye ne, kuma akwai hukuncin da dokar ta tanadar ga wanda ko bangaren da ya aikata haka.

KU KARANTA KUMA: Wasu masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da honarabul Hamzah M. Isah

”Dukkan mu mutane ne masu kima da mutunci. Daga bangaren majalisar har bangaren gudanarwar, duk mu na ga kima da sanin darajar dokoki dadin dadawa kuma duk mu na sane da rantsuwar da muka yi cewa za mu gudanar da ayyukan mu. Ka ga ashe a fannin zartarwa, idan ba su aiwatar da wadannan kudirorin da suka yi rantsuwa a kan su ba, sun san abin da doka ta tanadar musu.’’ Inji Dogara.

Dogara ya kara da cewa ai doka ta bada damar cewa a duk inda bangaren zartaswa ya ki aiwatar da wani kudiri wanda majalisa ta tabbatar da shi a matsayin doka, to alhakin majalisa ne ta tankwara bangaren zartaswa domin biyan bukatar al’umma.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras
NAIJ.com
Mailfire view pixel