Mata ta na jibga ta a duk lokacin da ta ji sha’awan yin haka – Inji Mijin tace

Mata ta na jibga ta a duk lokacin da ta ji sha’awan yin haka – Inji Mijin tace

- Toafeek Giwa ya koka ma wata kotun gargajiya dake zamanta a garin Agodi, jihar Ibadan

- Toafeek Giwa ya nemi da’a raba aurensu da matarsa Abiodun Omotayo

Wani dan fansho Toafeek Giwa ya koka ma wata kotun gargajiya dake zamanta a garin Agodi, jihar Ibadan, inda ya nemi da’a raba aurensu da matarsa Abiodun Omotayo.

Taofeek ya shaida ma kotu a ranar juma’a 16 ga watan Yuni, cewar matar tasa na jibgarsa ne ba kakkautawa ko da laifi ko ba laifi, kamar yadda kamfanin dillancin labaru ta ruwaito.

KU KARANTA: Kalli yadda aka dambace a majalisar jihar Nassarawa (Bidiyo)

A jawabinsa, Taofeek yace “Abu kadan sai kaga ta shiga jibga ta, har da yaga min riga, a yan kwanakin nan ma guba ta sanya min cikin abinci na, alhali kuma ban shirya mutuwa yanzu ba. Don haka nake bukatar kotu ta raba auren mu kafin ta kashe ni, domin in kula da yara na''

Mata ta na jibga ta a duk lokacin da ta ji sha’awan yin haka – Inji Mijin tace

Kotuu

Da take kare kanta, Uwargida Omotayo, ta musanta dukkanin zarge zargen da mijin nata yayi, inda tace asali ma mijin nata ne ke yawan binta da adda zai kashe ta, sa’annan tayi amanna da a raba auren, amma ta roki da bata dansu guda daya rak da suka haifa.

Ba tare da bata lokaci ba, kotu ta raba auren, sa’annan ta bata rikon dan nasu, daga bisani kotu ta umarci mijin daya baiwa matar N3000 duk wata domin kulawa da yaron nasu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rayuwar Hausawa a kudu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel