'Masu fasa-kwaurin kaya zuwa Najeriya zasu shiga halin tsaka mai wuya' - Comptroller Amajam

'Masu fasa-kwaurin kaya zuwa Najeriya zasu shiga halin tsaka mai wuya' - Comptroller Amajam

- An cafke motoci masu tsada da wasu kayayakin masarufi!

- Ana samun masu shigo da kaya ta barauniyar hanya

- Hukumar kwastan zata hada gwiwa da yan jarida don wayar da kan mutane

Masu fasakwaurin kaya zuwa Najeriya sun shiga halin tsaka mai wuya a yayin da hukumar customs din ta daura 'damara yaki da masu wannan muguwar sana'a. A halin yanzu za mu iya cewa wanka yafara biyan kudin sabulu domin hukumar karkashin sabon shugaban hukumar na Zone C a Owerri, Comptroller Amajam Bukar Alhaji sun sami gagarimin Nasara.

Comptroller Amajam Bukar Alhaji ya zaga da manema labarai a garuruwan Benin da Owerri idan ya nuna masu kayayyakin da hukumar tayi nasaran kwacewa a masu fasakwauri tun lokacin da haye kan mulki a watan mayun wannan shekaran zuwa yanzu, kayaya kin sun hada da;

'Masu fasa-kwaurin kaya zuwa Najeriya zasu shiga halin tsaka mai wuya' - Comptroller Amajam

'Masu fasa-kwaurin kaya zuwa Najeriya zasu shiga halin tsaka mai wuya' - Comptroller Amajam

1. Tayoyi (na hannu) guda 1591 wanda darajar kudin harajinsu ya kai N14,378,400

2. Buhunhunan shinkafa guda 3889 wanda darajan kudin harajinsu ya kai N101, 478, 000. An shigo da shinkafan ne a cikin motoci wanda sun hada da kirar Volkswagen, Volvo, Mercedes, Ford transit Bus da dai sauran su wanda darajar kudin harajinsu ya kai N19,740,300

3. Kwalayen sabulai guda 380 wanda darajar kudin harajinsu ya kai N10,093,009

4. Kwantaina mai girman 1x40ft da aka cafke a hanyan Aba/Eleme da ke dauke da abubuwa kamar kekunan dinki, gas cylinder, risho na girki, almakashi da dai sauransu wanda darajar kudin harajin nasu ya kai N111,572,300

5. Mota kirar Nisan Almera wanda darajar kudin harajin ta ya kai N4,725,000

Wannan ya kawo jimlar kudin harajin a N261,987,009.

Rundunar kuma ta karbo N10,646,477 a matsayin cikon kudaden da ba'a gama biya a cikin watan Mayu.

Wasu kayayakin da ke ajiye kafin a gama bincike a kansu sun hada da container mai dauke da yadin rolls wanda harajin sa ya kai N14, 100, 000 da kuma motoci na alfarma wanda suka hada da

6. 2016 Toyota Prado Jeep wanda harajin ta ya kai N17,348,647

7. 2011 Toyota Jeep wanda harajin ta ya kai N74,250,000

8. 2010 Mercedes Benz G-wagon Bullet Proof wanda harajinta ya kai N18,528,750

9. 2016 Range Rover wanda kudin harajinta ya kai N28,049,645.

A yayin da yake ganawa da manema labarai Comptroller Amajam yayi bayani cewa kayayakin da aka cafke sun karya dokokin 'kasa ne wanda suka hada da takurdun bogi da kuma yunkurin shigo da kayan ba tare da biya musu kudin haraji ba.

"Baza mu samu saukin kasuwanci ba idan babu gaskiya da amana a cikin lamarin, duk al'ummar da ke yin gaskiya da bin doka ne kawai zata samu saukin kasuwanci" Inji Comptroller Amajam

Ya kuma kara da cewa jama'a su daure su bi dokokin hukumar don samun saukin kasuwanci a kowane lokaci. Ya kuma cigaba da cewa rundunar zata cigaba da hadin gwiwa da yan jarida domin wayar da kan mutane akan ayukan hukumar.

Daga karshe sabon Comptrollan ya mika godiyar sa ga ma'aikatan rudunar da ke Zone C Owerri domin jajircewa da nuna hazaka wajen aiki. Kuma yayi kira da jama'a da su taimaka ma hukumar da bayanai masu amfani akan ayukan masu fasakwaurin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel