Wasu masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da honarabul Hamzah M. Isah

Wasu masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da honarabul Hamzah M. Isah

- Masu garkuwa da mutane sun sace wani dan siyasa na jihar Gombe

- Masu Garkuwa da mutanen sun saka shinge tare da sanya kayan Sarki a kan hanyar Kaduna zuwa zariya

- Sun sako shi bayan sun ajiye su a hannunsu na tsawon kwanaki biyu

Wasu masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da daya daga cikin matasan 'yan siyasa a jihar Gombe, Honorabul Hamza Muhammad Isah, wanda yake 'da ne ga Marigayi Alh. Muhammadu maigemu, wanda suke da zama a unguwar Bolari, a cikin garin Gombe.

Honarabul Hamza wanda tsohon kansila ne a unguwar Bolari, a halin yanzu yana daya daga cikin masu taimakawa gwamnan jihar Gombe a harkokin mulki (S.S.A.).

KU KARANTA KUMA: Kalli yadda aka ci mutuncin ɓarawon doya ɗan ƙabilar IboKalli yadda aka ci mutuncin ɓarawon doya ɗan ƙabilar Ibo

Wasu masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da honarabul Hamzah M. Isah

Honarabul Hamzah M. Isah

Masu Garkuwa da mutanen sun saka shinge tare da sanya kayan Sarki a kan hanyar Kaduna zuwa zariya, wanda suka tsaida shi, ba tare da wani bata lokaci ba suka dasa masa bindiga kirar AK47, suka nausa da shi cikin jeji suna tafiya, tun karfe shida na yamma har karfe dayan dare. Masu Garkuwa sun daure shi tare da masa wulakanci kala kala, bayan ya kwana biyu a wajen su, tare da kammala wasu abubuwa suka sako shi a jiya Alhamis.

Wasu masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da honarabul Hamzah M. Isah

Wasu masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da honarabul Hamzah M. Isah

Sai dai motar sa kirar Honda Crosstour kamar yadda kuke ganin hoton, har yanzu tana wajen su.

Wasu masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da honarabul Hamzah M. Isah

Wasu masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da honarabul Hamzah M. Isah

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel