Za a biya kusan N2miliyan ga wanda ya yarda a sa masa cuta

Za a biya kusan N2miliyan ga wanda ya yarda a sa masa cuta

- Shin nawa za a biya ka, don a yaɗa maka tarin fuka da gangan saboda gwajin kimiyya? Masu bincike a Jami'ar Southampton ta Ingila na tayin ba da ladan fam 3,526 kusan naira miliyan biyu kan wannan ƙalubale.

- Suna son yin wani ingantaccen riga-kafi don kare jarirai da yara 'yan dagwai-dagwai har ma da manyan da ke cikin kasadar kamuwa da wannan cuta.

- Don samun wannan dama, sai shekarun mutum sun kai 18-45 kuma sai mai ƙoshin lafiya wanda zai so zama a wani keɓantaccen wuri tsawon kwana 17 yana rera waƙa.

Tarin fuka, wata cuta ce mai saurin yaɗuwa ta hanyar tofar da yawu ko tari daga mutanen da suka kamu.

Ayarin ƙwararru a Southampton na son yaɗa wa mutane masu ƙoshin lafiya ƙwayar wannan cuta (ta hanyar ɗora ƙwayoyin bakteriyar da ake kira pertussis a kan hancinsa) don ganin yadda za su wanye.

NAIJ.com ta samu labarin cewa wasu daga cikin 'yan sa-kan za su kamu da rashin lafiya, amma masana kimiyyar sun fi mayar da hankali a kan waɗanda ba a ga kowanne nau'i na alamomin cutar a jikinsu ba, duk da yake, ƙwayar cutar ta shige su ta hanci.

Abin da suke nema a nan shi ne masu ɗauke da cutar a fakaice, da kuma mutanen da tun ainihi suna da kariyar wannan cuta mai yaɗuwa.

Za a biya kusan N2miliyan ga wanda ya yarda a sa masa cuta

Za a biya kusan N2miliyan ga wanda ya yarda a sa masa cuta

Mutanen da ke ɗauke da cutar a fakaice suna yaɗa cutar tarin fuka ga wasu, amma dai su kuma ba ta sa su rashin lafiya ba.

Ga alama suna da isasshen garkuwar cutar tarin, duk da yake ba a yi musu riga-kafi ba.

Akwai mutane ƙalilan, waɗanda su kwata-kwata ba sa kamuwa.

Fahimtar hakan za ta taimaka wajen ƙirƙiro wani riga-kafi mai matuƙar inganci.

Jagoran masu binciken, Farfesa Robert Read na cewa: "Muna son sanin wacce irin baiwa ce da su, kuma me ya sa ba za mu iya harbarsu da cutar ba, har su dinga yaɗa ta a fakaice."

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel