Kalli yadda aka dambace a majalisar jihar Nassarawa (Bidiyo)

Kalli yadda aka dambace a majalisar jihar Nassarawa (Bidiyo)

- An ga wani bidiyo dake nuna wasu yan majalisa suna fada da juna

- Yan majalisun sun fito ne daga majalisar jihar Nassarawa

Wani sabon faifan bidiyo daya mamaye shafukan yanar gizo ya nuna yadda wasu yan majalisu daga majalisar jihar Nassarawa suka dinga cusa ma juna naushi suna dambe.

NAIJ.com ta ruwaito wannan kazamin lamari ya faru ne sakamakon tirjiya da wasu yan majalisu su shidda suka nuna game da manufar gwamnan Jihar Al-Makura na nada sabbin shwuagabannin rikon kwarya a kananan hukumomin jihar.

KU KARANTA: Shari’ar Zakzaky ta fuskanci cikas a Kaduna

Yan majalisun sun nuna tirjiyar ne sakamakon rashin neman izininsu da gwamnan bai yi ba dangane da nadin shuwagabannin rikon.

Kalli yadda aka dambace a majalisar jihar Nassarawa (Bidiyo)

Yan majalisar suna dambe

Sai dai a wani sanarwa da yan majalisun su shidda da tuni aka dakatar dasu daga majalisar suka fitar, sun bayyana dalilin fadar su da cewa gwamna Tanko Al-Makura baya mutunta majalisar, inda suka zargi gwamnan da nada sabbin kantomomin ba tare da neman izinin majalisar ba kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.

“Ba zamu laminci wannan yi ma doka karan tsaye ba, kuma muna kira ga gwamna daya dakatar da wannan shiri nasa.” inji yan majalisun su shidda.

Ga bidiyon dakuwar nan:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel