Shari’ar Zakzaky ta fuskanci cikas a Kaduna

Shari’ar Zakzaky ta fuskanci cikas a Kaduna

- Lauyan wadanda ake kara yace, lauyan Zakzaky bai sanar da shi bayanan shari'ar ba

- Alkali mai shari'a ya dage sauraron karar suwa karshen wata

Wata yar tataburza ta wakana a cikin dakin sauraron shari’a na babban kotun tarayya dake zaune a jihar Kaduna yayin gabatar da shari’ar shugaban kungiyar yan Shi’a Malam Ibrahim El-Zakzaky, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A zaman kotun a ranar Alhamis 15 ga watan Yuni, inda yan shi’a suka shigar da hukumar Sojojin kasar nan da wasu bangarori guda uku da suka hada da shugaban rundunar sojin kasa, lauyan hukumar Soji Hussein Oyebanji yace bashi da masaniya akan karar da ke gaban kotu.

KU KARANTA: Ruwa ya karya gadoji a Adamawa, kalli yadda jama’a ke tsallaka rafi

Jin hakan yayi matukar baiwa alkali mai shari’a Saleh Shuaibu mamaki, inda yace “Ya za’ayi an sanya ranar sauraron karar amma ace lauyan wanda ake karaa bashi da masaniya akan tuhume tuhumen? Don haka zan dage sauraron karar domin baiwa lauyan damar samun dukkanin bayanan da suka dace.”

Shari’ar Zakzaky ta fuskanci cikas a Kaduna

Zakzaky

Daga nan sai mai shari’a Saleh Shuaibu ya dage sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Yuni.

Idan ba’a manta ba, a ranar 2 ga watan Disambar bara ne NAIJ.com ta ruwaito wata babbar kotu dake zamanta a Abuja ta bada umarnin a saki shugaban kungiyar shi’a Ibrahim Zakzaky.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Labarin wani tsohon sojin Biyafara:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel