Kalli yadda aka ci mutuncin ɓarawon doya ɗan ƙabilar Ibo

Kalli yadda aka ci mutuncin ɓarawon doya ɗan ƙabilar Ibo

- Wani mutum da aka kama da satar doya ya shiga tasku

- Mutumin yaci duka a hannun jama’a

Wani barawon doya ya gamu da fushin fusatattun jama’a inda suka ci mutuncinsa bayan sun lakada masa dan banzan duka, ta hanyar sanya shi ya rataya doyar daya sata a wuyarsa.

NAIJ.com ta ruwaito an kama wannan barawo ne a babbar kasuwar garin Onitsha, dake jihar Anambra.

KU KARANTA: Dukiyoyi sun salwanta a sabuwar rikicin ƙabilanci data ɓarke a Benuwe

Duk da cewa ba’a bayyana sunan barawon ba, kuma ya kasa bada gamsashshen dalilin daya sanya shi satar, amma wasu na ganin fatara da yunwa da kuma lalacewar tattalin arziki ne ya sanya shi sata.

Kalli yadda aka ci mutuncin ɓarawon doya ɗan ƙabilar Ibo

Barawon doya ɗan ƙabilar Ibo

A kwanan baya da suka gabata, mun kawo muku rahoto akan wata hukunci da babbar kotun jihar Oyo ta yanke ma wasu matasa hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda sun saci wayar N10,000.

Kalli yadda aka ci mutuncin ɓarawon doya ɗan ƙabilar Ibo

Barawon doya ɗan ƙabilar Ibo

Matasan da hukunci ya shafa sun hada da Alaba Akinola (30) Sarafa Babalola (25) Sola Kolawole (27) and Ibrahim Gbedeogun.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani hukunci ya dace da barayi?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel