Ganawar Osinbajo da dattawan Arewa da Kudu na iya zama taron shan shayi – Inji kungiyar matasan Arewa

Ganawar Osinbajo da dattawan Arewa da Kudu na iya zama taron shan shayi – Inji kungiyar matasan Arewa

Rahotanni sun kawo cewa an bayyana ganawar da Mukaddashin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osibanjo ya yi da shugabannin yankin Arewa da na kudu, a matsayin wani mataki da ya dace amma a bangare daya yana iya zama taron shan shayi, idan har ya zamana ba'a dauki matakan da suka dace ba na warware salsalan rikicin.

Hakan na fitowa ne daga bakin daya daga cikin Shugabannin gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa 16 da suka bada wa'adin watannin uku ga dukkanin yan kabilar Igbo dake Arewacin kasar

Alhaji Sharrif ya kara da cewa babu wani babba daga yankin Kudu maso gabas da ya fito ya soki lamirin abinda tsagerun yankin karkashin jagorancin Nnamdi Kanu suke yi, face yaba musu da kuma mara musu baya.

KU KARANTA KUMA: Kalli yadda aka ci mutuncin ɓarawon doya ɗan ƙabilar IboKalli yadda aka ci mutuncin ɓarawon doya ɗan ƙabilar Ibo

Don haka ganawar su da Mukaddashin Shugaban kasa na iya zama aikin Baban Giwa, kasancewar tsofaffin na yankin Igbo na ba tsaegurun matasan su goyon baya dari bisa dari , saboda haka kamata ya yi Shugabannin Kasa suyi zama kuru-kuru da Matasan Igbo domin suyi bayani na zaba cikin biyu Najeriya ko Biyafara.

Ganawar Osinbajo da dattawan Arewa da Kusu na iya zama taron shan shayi – Inji kungiyar matasan Arewa

Ganawar Osinbajo da dattawan Arewa da Kusu na iya zama taron shan shayi, Inji kungiyar matasan Arewa

Dangane da ziyarar da tsohon Dogarin tsohon Shugaban Kasa Marigayi Sani Abacha wato Manjo Hamza Al Mustafa mai ritaya ya kawo kwanakin baya a garin Kaduna, inda ya gana da wasu daga cikin shugabannin Igbo Ashir Shariff ya tabbatar da cewar su a matsayinsu na shugabannin Kungiyoyin Matasan Arewa ba su aiki kowa ya gana da yan kabilar Igbo ba, haka kuma su a matsayinsu na wadanda suka yi wancan magana ta bayar da wa'adin korar Inyamurai babu wanda ya gayyace su wannan taro, wanda hakan ya nuna cewar da akwai akasi kenan

Sannan kuma yan yankin Kudu sun san su waye Matasan Arewa, kuma sun san hanyar da zasu nemi ganawa dasu, amma sai su kayi kwana suka gana da Al Mustafa, wanda hakan ke gwada cewar sun bar Jaki da gangan sun koma dukan taiki kenan.

Kungiyar Matasan Arewan sun kara da cewar, ko kadan ba su da bukatar cigaba da zama da Inyamurai a tarayyar Najeriya muddin Inyamuran na cigaba da nuna kyama da wariya ga Jama'ar Arewa, sannan lallai ne Shugaban Kasa ko Mataimakin shi suyi zama a fili da Matasan Igbo su furta da bakin su suna bukatar cigaba da zama a Najeriya ba wai an yi musu dole ba ne, kuma duk wanda suka zaba a ciki Kungiyar Matasan Arewa na marhabin da shi ba tare da wani jinkiri ba.

Matasan Arewan sun kuma tabbatar da cewar wannan fafutuka da suke yi na neman 'yancin Jama'ar Arewa su nayi ne bakin rai bakin fama, kuma basu shakkar dukkanin wani bara gurbi dake da mukami a Arewa wanda zaiyi barazanar kama su ko kuma wasu tsofaffi da zasu ki mara musu baya, domin ko an ki ko an so dole sune zasu gaji Arewa, wadancan tsofaffi tasu ta riga ta kare, saboda haka ya dace suyi shiru shine alkhari a garesu.

Daga karshe Matasan sun bayyana cewar za suyi wani gagarumin taro a ranar Talata mai zuwa a garin Kaduna domin kara fito da matsayinsu akan dukkanin wani Inyamuri ko wani bara gurbi a yankin Arewa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel