Taƙaddama ta ɓarke tsakanin Sanatoci da shugaban hukumar Hajj ta ƙasa (Hotuna/Bidiyo)

Taƙaddama ta ɓarke tsakanin Sanatoci da shugaban hukumar Hajj ta ƙasa (Hotuna/Bidiyo)

- An tada jijiyar wuya tsakanin Sanatoci da shugaban hukumar Hajj

- Sa'in'san ya faru ne sakamakon tsadar farashin Hajji

Batun tsadar farashin kujerar Makkah na bana na cigaba da tada hazo a farfajiyar siyasar Najeriya, musamman daga bangaren Musulmai wadanda abin ya shafa.

Gidan rediyon BBC Hausa ya samu wani faifan bidiyi dake nuna yadda aka yi musayar yawu a tsakanin shugaban hukumar Hajji ta kasa Alhaji Abdullahi Mukhtar tare da wasu Sanatoci su biyu.

KU KARANTA: Shigar banza: Jama’a sun yi caa akan wata budurwa, ta sha da kyar

Sanatocin sun hada da Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba da Sanata Isa Hamma Misau, inda suka ce sam ba zata sabu ba, wai bindiga a ruwa.

Taƙaddama ta ɓarke tsakanin Sanatoci da shugaban hukumar Hajj ta ƙasa (Hotuna/Bidiyo)

Sanatoci da shugaban hukumar Hajj ta ƙasa

Ga dai bidiyon kamar yadda majiyar NAIJ.com ta kawo shi.

Idan ba’a manta ba dai tun bayan sanar da farashin kudin aikin Hajji na bana ne aka dinga cece kuce musamman saboda tsadar farashin, kamar yadda Musulmai yan Najeriya suke kokawa.

Farashin aikin Hajji na bana ya kai Naira miliyan daya da dubu dar biyar ga duk maniyyaci (1,500,000), sai dai shugaban hukumar Hajjin yace dalilin tashin goron zabin da farashin yayi shine tsadar dala.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana yunkurin tsige wani Sanata

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel