Ramadan: Kwanaki 10 kafin Sallah, Sanatoci sun tafi hutu

Ramadan: Kwanaki 10 kafin Sallah, Sanatoci sun tafi hutu

- A yau, kimanin kwanaki 10 kenan kafin Sallah, Sanatoci sun fara hutu

- Sanatocin sun debi hutun satuka guda 3 ne

A ranar Alhamis 15 ga watan Yuni ne yan majalisar dattawa suka dage zaman majalisa har sai bayan satuka guda uku, domin yin hutun karamar Sallah da kuma na murnar cikarsu shekaru 2.

Jaridar Daily Post ta ruwaito a ranar juma’a 9 ga watan Yuni ne dukkanin majalisun biyu, na wakilai da dattawa suka cika shekaru 2 cig cif da kama madafan iko, inda kuma suma gudanar da wata yar kwarya kwaryar zama domin murnan wannan rana.

KU KARANTA: Saurayi ya hallaka budurwarsa saboda tayi jinkirin wanke masa kaya

Zaman ya smau halartan jiga jigan majalisar daga dukkanin bangarorin biyu, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta kalato.

Ramadan: Kwanaki 10 kafin Sallah, Sanatoci sun tafi hutu

Sanatoci

Bugu da kari dayake ana sa ran a ranakun 25 da 26 ne za’a yi bikin karamar Sallah bayan watan Ramadana, yan majalisun sun tattara hutun nasu har sai bayan sallar.

Bayan kammala zaman majalisar ne, sai shugaban masu rinyaje, Ahmad Lawan ya gabatar da kudirin dage harkokin majalisa har sai bayan sati uku, daga nan kuma shugaban marasa rinjaye Akpabio ya mara masa baya.

Shikenan sai shugaban majalisar Sanata Bukola Saraki ya buga guduma, alamar an tashi zaman kenan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin majalisar dattawa nada amfani kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel