An kama yan Najeriya dake fashi da makami a Ghana (HOTUNA)

An kama yan Najeriya dake fashi da makami a Ghana (HOTUNA)

- An kama wasu yan Najeriya da suka kware a sana’ar fashi da makami

- Matasan sun shiga hannu ne a kusa da fadar shugaban kasar Ghana

Wasu rahotanni sun bayyana cewa a ranar Laraba 14 ga watan Yuni ne aka kama wasu yan Najeriya da suka kware a muguwar sana’ar nan ta fashi da makami a kasar Ghana.

Dubun yan fashin ta cika ne yayin da yansanda suka yi caraf dasu a lokacin da suke yin fashi a gab da fadar shugaban kasar Ghana, a wannan karo, yan fashin sun tare wani mutumi ne inda suka kwace masa kimanin N400,000 a kudin kasar Ghana.

KU KARANTA: Saurayi ya hallaka budurwarsa saboda tayi jinkirin wanke masa kaya

Majiyar NAIJ.com ta bayyana sunayen yan fashi da Ndubueze Odoemenam da Chiokoko Amadie dukkaninsu yan kabilar Ibo kamar yadda kwamandan rundunar yansanda ya shaida mata.

An kama yan Najeriya dake fashi da makami a Ghana (HOTUNA)

Yan fashin

Yan fashin sun yi amfani da dabarar fasa tayar mota ne akan mutumin da suka aikata ma fashin, sai dai wani mutumi daya lura dasu, ya bisu da gudu a babur dinsa, a haka ne jama’a suka yi musu a tara tara, har suka cin masu.

Nan da nan, ba tare da bata lokaci ba, jama’a suka diran musu da duka, inda suka farfasa musu bakuna tare da kumbura musu fuskoki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ta yaya ya kamata a hukunta barayi?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel