Ra'ayoyin ‘yan Najeriya kan wanke shugaban majalisar dattijai da kotu tayi

Ra'ayoyin ‘yan Najeriya kan wanke shugaban majalisar dattijai da kotu tayi

- Ra’ayi ya sha bam-bam tsakanin wakilan majalisa tarayyar dangane da wanke Bukola Saraki

- Gwamnatin tarayya ta shigar kan shugaban majalisar dattijan na kin bayyana dukiya ko kadaroinsa

- Senata Sabbi Abdullahi ya ce Allah ya wanke bawansa wato Bukola Saraki

- Ahmed Babba Kaita ya ce akwai bukatar a sake nazarin yadda ake tafiyar da harkokin shari’a a kasar

Ra’ayoyin ‘yan Najeriya sun sha bam-bam tsakanin wakilan majalisa tarayya dangane da wanke shugaban majalisar dattijan Najeriya Bukola Saraki.

A makon nan ne kotun da’a wacce take sauraron karar da gwamnatin tarayya ta shigar kan shugaban majalisar dattijan na kin bayyana dukiya ko kadaroinsa ta wanke shi.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, mai magana da yawun majalisar dattijai, Senata Sabbi Abdullahi ya ce “Allah ya wanke bawansa, amma wadanda tun farko suka hakikance cewa, Bukola yana da laifi ba zasu daddara ba."

Ra'ayoyin ‘yan Najeriya kan wanke shugaban majalisar dattijai da kotu tayi

Shugaban majalisar dattijan Najeriya, sanata Bukola Saraki

A nasa bangaren Suleiman Nazif, ya bayyana farin cikin wannan hukunci, yana mai cewa, suna yiwa “Allah godiya”. Kuma suna tare da shugaban na su dari bisa dari.

KU KARANTA: Damuwata ta kau kan wanke ni da kotu ta yi — Saraki

Sai dai dan majalisar wakilai Hamma Isa Misau yace, tun fara shari’ar ya hangi cewa akwai matsala, domin akwai alamar karya aka kwantarawa senata Saraki.

Amma Ahmed Babba Kaita, yace akwai bukatar a sake nazarin yadda ake tafiyar da harkokin shari’a, ta yadda za’a gudanar da adalci, maimakon karkata hukunci saboda mukamin mutum.

Wani dan jam’iyyar APC, mai mulkin kasar, Khalid Isma’il, yayi kira ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya binciki bangaren shari’a saboda tabbatar da adalci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Mazabar jihar Kogi ta yamma zata yi zaben dawo da Sanata Dino Melaye daga majalisar dattijai

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel