Rikici: Ministan Shari’a ya shiga matsala bayan Kotu ta wanke Bukola Saraki

Rikici: Ministan Shari’a ya shiga matsala bayan Kotu ta wanke Bukola Saraki

– Kotu ta wanke Shugaban Majalisar Dattawa Saraki

– Hakan ta sa wasu Jama’a su ka fara kira a salami Ministan shari’a

– Yanzu dai Abubakar Malami na cikin matsala

Wani tsohon Shugaban Lauyoyin Najeriya yayi tir da abin da ya faru. Jama’a dai sun hurowa Ministan shari’a Abubakar Malami wuta. Haka kuma kwanaki aka maido Alkalan da ake zargi da laifi.

Rikici: Ministan Shari’a ya shiga matsala bayan Kotu ta wanke Bukola Saraki

Ministan Shari’a ya shiga matsala

Tsohon Mataimakin Shugaban Lauyoyin Najeriya watau NBA Monday Ubani yayi tir da nasarar da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya samu a Kotu inda yace Najeriya ce za tayi kuka ba kowa ba.

KU KARANTA: An yi wa Ahmed Musa nadin sarauta

Bayan haka ne ma dai aka yi kira ga Ministan shari’ar kasar Abubakar Malami SAN da kuma Alkali mai shari’a Danladi Umar su sauka daga kujerun su don kuwa sun gaza. Alkali Danladi Umar na Kotun CCT ya wanke Saraki kal kamar yadda Mahaifiyar sa ta haife sa.

Haka shi ma Tsohon Ministan Neja-Delta lokacin Shugaba Goodluck Jonathan watau Godswin Elder Orubebe ya sha a Kotu inda aka wanke sa tas daga zargi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Magana game da kasafin kudi a Najeriya [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin Zamfara za ta samu kimani biliyan 56 daga asusun gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel