'Kura-kuran Buhari ne suka durkusar da Najeriya' - Reno Omokri

'Kura-kuran Buhari ne suka durkusar da Najeriya' - Reno Omokri

- Buhari ya kashe ayyuka miliyan 4 a wata uku

- Ya tsayar da dukiyar kasa cak

- Ya talauta Najeriya dare daya

- Buhari yayi satar amsa daga tsohon shugaba Jonathan

A sabuwar caccaka da ya saba fitarwa kusan kullum kan gwamnatin APC, Reno Omokri, tsohon hadimin shugaba Jonathan mai zama a Amurka, ya ce dare daya Buhari ya talauta Najeriya, saboda kawai ya matsu ya nuna bajintarsa.

A cewarsa, yana hawa mulki, shugaba Buhari ya dauki matakin kwakwashe duk kudin kasa ya boye a babban bankin Najeriya, na CBN, inda ya talauta dukkan ma'aikatu. Wannan shine ummul-aba'isin durkushewar Najeria dare daya.

KU KARANTA KUMA: Kalli yadda aka ci mutuncin ɓarawon doya ɗan ƙabilar IboKalli yadda aka ci mutuncin ɓarawon doya ɗan ƙabilar Ibo

'Kura-kuran Buhari ne suka durkusar da najeriya' - Reno Omokri

'Kura-kuran Buhari ne suka durkusar da najeriya' - Reno Omokri

A cewar Reno, shawarar tare dukiyar kasa wuri daya ta tsohuwar ministar kudi ne, Okonjo-Iweala, da Goodluck Jonathan, amma su a hankali suke niyyar yi ba dare daya ba.

"Kwashe kudaden, shi ya kawo durkushewar Najeriya dare daya, ya kuma kawo korar ma'aikata miliyan hudu da rabi," inji shi.

A cewarsa, hukumar kididdiga ta kasa ta bayar da kiyasin rasa ayyukan yi har dubu hamsin daga bankuna kadai, saboda kudadensu na kasuwanci da aka kwashe.

An dai sami matsalolin tattalin arzikin kasa sosai a shekaru biyu na mulkin APC.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel