Najeriya ta kuduri anniyar kwato kayayyakin tarihinta da aka sace zamanin mulkin mallaka

Najeriya ta kuduri anniyar kwato kayayyakin tarihinta da aka sace zamanin mulkin mallaka

- Ministan yada Labarai, Lai Mohammed ya bada tabbacin cewa za’a kwato kayan tarihin Najeriya daga kasashen ketare

- Wasu kasashen ketare tuni sun maido da kayayyakin tarihinta da ke kasar su

- Malama Jeane ta bayyana cewa abin takaicin ne ganin 'yan Najeriya basa sha'war karatu kan dadaddun kayan tarihi

Ministan yada Labarai na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana kudurin gwamnatin tarayyar Najeriya na ci gaba da fafutukar ganin ta kwato dukkan kayayyakin tarihi da aka sace daga kasar zamanin mulkin mallaka zuwa kasashen waje.

A jawabinsa, ministan ya gayawa mahalarta bikin nuna kayyakin tarihi da aka yi a Legas cewa, gwamnati tana basu tabbacin cewa ba zata yi kasa a guiwa ba wajen ganin dukkan kayyakin tarihinta da aka kai kasashen yammacin duniya da kuma Amurka an dawo da su.

Ita ma a nata jawabin wata 'yar kasar Amurka Malama Jeane, wacce take karantar da kayayyakin tarihi a jami'ar Benin, ta bayyana takaicin ganin 'yan Najeriya basa sha'war karatu kan dadaddun kayan tarihi, sun gwammace na zamanin yau.

Najeriya ta kuduri anniyar kwato kayayyakin tarihinta da aka sace zamanin mulkin mallaka

Ministan yada Labarai na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed

KU KARANTA: Dubi abin da aka ga wani Ministan Buhari yake yi a gida

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, sugaban hukumar da take kula, da kuma adana kayayyakin tarihi Alhaji Yusuf Abdullahi Usman, yayi karin haske kan kasashe shida ciki harda Amurka da Faransa, wadanda suka maidowa Najeriya kayayyakin tarihinta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rotimi Amaechi ya bayyana jerin ayyukan da gwamnatin shugaba Buhari ya yi a mulki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel