Dalilin da ya sa El-Zakzaky ke a tsare har yanzu – Lai Mohammed

Dalilin da ya sa El-Zakzaky ke a tsare har yanzu – Lai Mohammed

- Ibrahim El-Zakzaky na a tsare tare da iyalinsa da ma wasu manyan mabobi kusan sama da shekara daya bayan wani karo da hukumar sojin Najeriya

- Lai Mohammed, ministan bayanai da al’adu, ya ce baya tsare amma yana karkashin kulawa

Ministan bayanai, Lai Mohammed, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da tsare shugaban kungiyar ‘yan shi’a Ibrahim El-Zakzaky ne saboda har yanzu bata sama masa gida ba.

A cewar ministan, kotu ta bada umurnin sakin El-Zakzaky bayan an gina masa sabon gida.

Ya yi bayanin cewa babu wani an kasar da zai amince da shi a matsayin makwabci, ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta yanke hukunci ajiye shi a guri mai tsaro a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Bayan auren sabuwar mata, an nada ma Ahmed Musa sarauta

Dalilin da ya sa El-Zakzaky ke a tsare har yanzu – Lai Mohammed

Lai Mohammed, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da tsare shugaban kungiyar ‘yan shi’a Ibrahim El-Zakzaky ne saboda har yanzu bata sama masa gida ba

Mohammed ya kara da cewa, shugaban kungiyar wanda hukumar soji ta kama a watan Disamba na shekarar 2015 baya gidan yari ko hannun hukumar DSS.

A maimakon haka, ya ce El-Zakzaky na karkashin kulawa tare da iyalinsa, ya kara da cewa gwamnatin tarayya bazata iya kin bin umurnin kotu ba dangane da shugaban na kungiyar Shi’a da tsohon mai ba kasa shawara a harkan tsaro, Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya).

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com don ganin yadda abunda yan Najeriya ke fadi game da Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel