'Yan tada kayar bayan Neja Delta sun baiwa jama'ar Arewa wa'adin fice wa daga yankinsu

'Yan tada kayar bayan Neja Delta sun baiwa jama'ar Arewa wa'adin fice wa daga yankinsu

- Kungiyar tsagerun Niger Delta sun ce zasu kona rijiyoyin mai na 'yan arewa

- Sun ce an kasa kama samarin arewa

- Sannan kuma sun sha alwashin kafa tasu kasar

Hadakar kungiyoyin mayakan Neja Delta ta tashi daga taron ta na kasa a jihar Ribas, inda ta yanke kudurin baiwa mutanen arewa mazauna kudu wa'adin zuwa watan Oktoba, da su tattara nasu-ya nasu su bar musu yankinsu, sun kuma ce duk wani dan arewa mai rijiyar mai ya dena sha musu mai.

Mayakan, sun kuma caccaki shugaban kasa Osinbajo da shugaban yan-sanda da ma hukumomin soji da na DSS, kan kasa kame samarin arewa da suka baiwa na kudu wa'adin barin arewa.

KU KARANTA KUMA: Abin kunya: Saudi ta aikowa Najeriya dabino sadaka amma an saida

'Yan tada kayar bayan Neja Delta sun baiwa jama'ar Arewa wa'adin fice wa daga yankinsu

'Yan tada kayar bayan Neja Delta sun baiwa jama'ar Arewa wa'adin fice wa daga yankinsu

Mayakan da suka rattaba hannu kan shawarar, sun hada da; Janar John Duku (Niger Delta Watchdogs); Janar Ekpo Ekpo (Niger Delta Volunteers); Janar Osarolor Nedam (Niger Delta Warriors); Manjo-Janar Henry Okon Etete (Niger Delta Peoples Fighters); Manjo-Janar Asukwo Henshaw (Bakassi Freedom Fighters); Manjo-Janar Ibinabo Horsfall (Niger Delta Movement for Justice); Manjo-Janar Duke Emmanson (Niger Delta Fighters Network); Manjo-Janar Inibeghe Adams (Niger Delta Freedom Mandate); da kuma Manjo-Janar Ibinabo Tariah (Niger Delta Development Network).

"Taron da mukaddashin shugaban kasa yayi ya bamu kunya, inda maimakon ya kame su sai kawai ya bige da basu hakuri da zaman lafiya, wannan munafunci ne," inji sanarwar.

Ana dai kallon wannan yunkuri a matsayin martani da ka iya balla kasar najeriya muddin ba'a shawo kan batun da wuri ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel