Ramadan: Gwamnatin Kano ta ciyar da musulmi 930,000

Ramadan: Gwamnatin Kano ta ciyar da musulmi 930,000

- Gwamnatin Jihar Kano ta ciyar da kimani mutane 930,000 a cikin watan Ramadan har zuwa yanzu

- Mutane 250 ne gwamnati ke ciyarwa kullum a lokacin bude baki daga kowace cibiyoyin 186 da ke fadin jihar

- Gwamnatin jihar zata ciyar da mutane fiye da miliyan 1.395 a wannan watan Ramadan

Gwamnatin Jihar Kano ta ciyar da kimani musulmai 930,000 tun daga ranar farkon azumin watan Ramadan zuwa yanzu.

Shugaban kwamitin Ciyarwa na watan Ramadan kuma kwamishinan Labarai, Malam Muhammad Garba ya bayyana wannan lokacin da yake jawabi ga manema labarai a gidan gwamnatin jihar Kano a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni.

Ya ce mutane 250 ne gwamnati ke ciyarwa kullum a lokacin bude baki daga kowace cibiyoyin 186 da ke fadin jihar gaba daya.

Ramadan: Gwamnatin Kano ta ciyar da musulmi 930,000

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umaru Ganduje na gaisawa da al'ummarsa

"Ciyar da mutane 250 daga kowace cibiyoyin 186 zai bamu kimani mutane 46,500 a kowace rana, kuma idan aka hada da kwana 30 na watan Ramadan, samu kasance da mutane fiye da miliyan 1.395 wadanda za a ba abinci" Inji kwamishinan.

KU KARANTA: Hotuna 3 da za su ba ka mamaki game da Minista Amaechi Read

NAIJ.com ta ruwaito cewa, Garba ya yaba da kokarin gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Ganduje wajen tabbatar da cewa an ci gaba da ciyar da mutane a watan Ramadan wanda gwamnati ta saba shekara da shekara duk da koma bayan tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

Kwamishinan ya bayyana cewa kwamitin har ila yau ta samu nasarar a wannan shirin.

A cewar shi, gwamnatin jihar ta amince da ƙarin wasu kayyakin abinci ciki har da Spaghetti da Macaroni da sauran abubuwa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Gwamnan Fayose ya ce zai fafata da shugaban kasa Muhammadu Buhari a zben 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel