Sanata Shehu Sani ya roki iyalan Kasimu Yero bayan nuna rashin jin dadinsu kan hotunan da ya dauka da mahaifinsu

Sanata Shehu Sani ya roki iyalan Kasimu Yero bayan nuna rashin jin dadinsu kan hotunan da ya dauka da mahaifinsu

- Iyalan tsohon dan wasan kwaikawo Kasimu Yero sun nuna fushin su matuka kan hotunan mahaifinsu da Sanata Shehu Sani ya sa a yanar gizo

- Iyalan dan wasan sun ce abinda Sanatan ya yi bai yi daidai ba ganin halin da mahaifinsu ke ciki

- Sanata Shehu Sani ya ce ya ziyarci Kasimu Yero domin sada zumunta amma ba da wata niya na daban ba

Iyalan tsohon dan wasan kwaikawo Kasimu Yero sun nuna fushin su matuka kan hotunan mahaifinsu da Sanata Shehu Sani da wadansu suka saka a shafukan su na Twitter da Instagram bayan ya ziyarce shi a gidansa dake Unguwar Marafa.

KU KARANTA KUMA: Hotuna 3 da za su ba ka mamaki game da Minista AmaechiHotuna 3 da za su ba ka mamaki game da Minista Amaechi

Iyalan dan wasan sun ce abinda Sanatan ya yi bai yi daidai ba ganin halin da mahaifinsu ke ciki kuma su kayi ta daukanshi hotuna a haka sannan suka saka a shafin su na yanar gizo.

Kasimu Yero da aka fi sanin shi a wasanni kamar ‘Magana Jari Ce’ na fama da rashin lafiya a dan kwanakin nan.

Sanata Shehu Sani ya roki iyalan Kasimu Yero bayan nuna rashin jin dadinsu kan hotunan da ya dauka da mahaifinsu

Kasimu Yero

Sanata Shehu Sani ya saka hotunan shi tare da Kasimu Yero a yanar gizo bayan ya ziyarce shi a gidansa dake Marafa Kaduna ranar Lahadi.

Sanatan ya ce ya yi hakan ne da kyakkyawar manufa amma ba wai don ya tozarta shi ba.

Kuma ya ce sun yi hira sosai akan ayyukkansa da ya yi a aikin talabijn.

KU KARANTA KUMA: Tattalin arziki: Biliyan talatin mutan Najeriya suka kashe a Umarar bana

Wasu daga cikin ‘yan uwan Kasimu Yero sun yi matukar fusata lura da suka yi da cewa shi kansa sanatan ya saka hotunan a shafinsa mai makon ace wai shine ma zai yi hani akan haka.

A wata takarda da wani mataimakin Sanatan ya fitar sakamakon korafe-korafe dangane da abin da ya faru Suleiman Ahmed ya ce Sanata Shehu Sani ya ziyarci Kasimu Yero domin sada zumunta amma ba da wata niya na daban ba.

A bayanin da ya yi ya ce, “Mun ziyarci Kasimu Yero ne tare da ma’aikatan gidan jaridar Daily Trust da Rariya da kuma daya daga cikin yar sa kuma mun yi hira ne akan ayyukkan sa da ya yi na wasan kwaikwayo.

”Kasimu Yero ya nemi da Sanata Shehu Sani ya dauki nauyin sake shirya irin shirin Magana jarice domin yaran yanzu su ga yadda al’adar Hausa take tuna da. Daga nan ne sanata ya shawarci Kasimu Yero da ya rubuta bayanai akan abubuwan da ake bukata inda shi kuma zai samo wadanda zasu dauki nauyin yin hakan."

Ana shi bayanin da yayi ta da aka dauka ta naurar daukar Magana Kasimu Yero a bai san cewa wai ana daukarsa hutuna a inda yake ba. Amma ya tabbatar da ziyarar Sanata din da kuma hirar da sukayi akan sabunta shirin Magana Jari Ce.

“Bayan mun tattauna da Sanata da zai tafi kuma sai ya dauko naira 100,000 ya bani sannan nayi masa godiya amma ban ce ma wani ya taimakeni da kudi ba kamar yadda ‘ya’ya na suka sanar mini cewa wai har an saka hutunana a shafaunan sadarwa a yanar gizo wai ina neman taimako.”

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel