Damuwata ta kau kan wanke ni da kotu ta yi — Saraki

Damuwata ta kau kan wanke ni da kotu ta yi — Saraki

- Kotun kula da da'ar ma'aikata ta kasar ta wanke Saraki kan tuhuma da ake masa na kin bayyana kadarorinsa

- Shugaban majalisar dattawan ya yi jawabin jin dadi bayan an wanke shi

- Ya ce yanzu duk wata damuwarsa ta kau

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki ya yi jawabi bayan wanke shi da kotun kula da da'ar ma'aikata ta kasar ta yi, kan tuhumar da ake masa ta kin bayyana gaskiyar kadarorin da ya mallaka.

A jawabin da ya mayar a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya ce: "A yau 14 ga watan Yunin shekarar 2017, kotun kula da da'ar ma'aikata, wacce ta yi zamanta a Abuja, ta wanke ni a kan tuhumar da ake min, na boye wasu kadarori da na mallaka, wadda aka fara shari'ar a watan Satumbar 2015".

KU KARANTA KUMA: Tattalin arziki: Biliyan talatin mutan Najeriya suka kashe a Umarar bana

Damuwata ta kau kan wanke ni da kotu ta yi — Saraki

Bukola Saraki ya bayyana ce wa duk wata damuwarsa ta kau kan wanke shi da kotu ta yi

Sanatan ya kara da cewa: "Idan ba ku manta ba, a farkon fara shari'ar, na bayyana cewar ban yi wani laifi ba, kammala wannan shari'ar ya tabbatar da matsayina, yadda aka tafiyar da shari'ar ya kara mana karfin gwiwar cewa, bangaren shari'a shi ne wuri na karshe da ke samar da adalci ga kowa".

Ya ci gaba da cewa: "Bayan fusakantar shari'a mai wahala, wanke nin da aka yi a yau, ya yaye min dukkan wata damuwa, kuma ban riki kowa a zuciyata ba, duk da irin muzgunawar da na fuskanta a tsawon lokacin da aka shafe ana shari'ar."

Sai dai kuma har zuwa yanzu bangaren gwamnatin tarayya da ta shigar da karar ba su komai ba kan hukuncin da kotun ta yanke.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel