Amnesty ta ce tana kan bakarta a kan sojin Najeriya

Amnesty ta ce tana kan bakarta a kan sojin Najeriya

- Amnesty International ta jadadda matsayin ta kan sojin Najeriya

- kwamitin na musamman da rundunar sojin Najeriya ta kafa ta wanke sojojin kasar da ake zargi da cin zarafin bil’adama

- Amnesty ta ambaci sojoji 6 da ta bukaci a hukunta kan aikata laifuka da suka shafi kisa da azabtar da mutane

Wani kwamiti na musamman da rundunar sojin Najeriya ta kafa ya wanke sojojin kasar da ake zargi da cin zarafin bil’adama a yankin arewa maso gabashi da kuma kudu maso gabashin kasar.

Rundunar sojin Najeriya ta ce babu hujjoji da suka tabbatar da zargin da ake wa kwamandojinta.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta fitar da rahoto mai shafi 133 a watan Yunin 2015 da ke zargin sojojin Najeriya da kashe mutane da sunan Boko Haram da kuma kashe masu fafatukar kafa kasar Biafra.

Amnesty ta ce tana kan bakarta a kan sojin Najeriya

Sojojin Najeriya

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Amnesty ta zargi sojin da cin zarafin bil’adama tare da amfani da karfin da ya wuce kima kan jama’a.

Har yanzu dai Amnesty ta ce, tana nan kan bakarta.

KU KARANTA: 'Nasarar Bukola Saraki ta Karyata shugaba Buhari' inji Reno Omokri

Rahoton kwamitin na musamman da rundunar sojin Najeriya ta kafa ya nuna kamar mai laifi ne ya wanke kansa.

Rahoton Amnesty ya zayyana sojoji 6 da ta bukaci a hukunta kan aikata laifuka da suka shafi kisa da azabtar da mutane da sunan yaki da Boko Haram.

Rahoton Amnesty ya yi zargin cewa sama da mutane 1,200 sojojin suka kashe, tare da cafke dubban mutane yadda suka ga dama.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a lokacin da yake kaddamar da aikin hanyan jirgin kasa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel