Tsutsa na cinye shukar manoma a sassan Najeriya

Tsutsa na cinye shukar manoma a sassan Najeriya

- Wata tsutsa mai cin hatsi ta mamaye gonakin mutanen a jihohi daban-daban a Najeriya

- Alhaji Sanusi Muhammad ya ce tsutsar ta yi mummunar barna a gonaki musammam waɗanda shukarsu ba ta yi ƙwari ba

- Muhammad ya ce zancen a ce za a yi wa tsutsan feshi bata lokaci ne

Wata tsutsa da ke mamaye gonaki ta fantsama kan shukar manoma musammam amfanin gona irinsu masara da gero da dawa da shinkafa a wasu sassa na Najeriya.

Jami'ai sun ce matsalar ta fi ƙamari a jihohin Binuwai da Neja da Katsina da Oyo da kuma bayan-bayan nan Zamfara da Kano.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, sakataren ƙungiyar manoman shinkafa shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, Alhaji Sanusi Muhammad Gusau ya ce tsutsar ta yi mummunar barna a gonaki musammam waɗanda shukarsu ba ta yi ƙwari ba.

Tsutsa na cinye shukar manoma a sassan Najeriya

Tsutsan da bata jin feshin magani

A cewarsa tsutsar ta fi ɓarna a yankin tsakiyar Zamfara, ciki har da Gusau da Bungudu da Maru da Tsafe.

Ba ta damu da waken suya ko kuma tafasa ba ta fi cin shukar shinkafa da sauran amfanin hatsi.

Ya ce irin yawan tsutsar, zancen a ce za a yi feshi ma, bata lokaci ne kawai.

KU KARANTA: YANZU YANZU: APC ta kori Jibrin, dan majalisa da aka dakatar

Sakataren Manoman ya ce ana cikin mawuyacin hali saboda maganar feshin magani ma bai taso ba, kuma har yanzu ba su iya samun wani tallafin gwamnati ba.

Shi ma wani masani kan harkokin tsirrai a Oyo ya ce kashi 90 cikin 100 na gonakin masara da suka ziyarta a jihar, tsutsar ta addabe su kwarai da gaske.

Alhaji Sanusi Gusau ya ce tuni har wasu manoman da tsutsar ta cinye wa gonaki suka fara sake wata shukar, don kuwa a cewarsa tsoffin da suka san tsutsar sun ci idan ruwa ya sauka sosai za ta tafi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Farashin kayan abinci a wasu kasuwanni a cikin wannan bidiyon

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel