Inyamurai: Mun yi hakuri haka ko matar kace ta nemi saki ai sai ku rabu-Ango Abdullahi

Inyamurai: Mun yi hakuri haka ko matar kace ta nemi saki ai sai ku rabu-Ango Abdullahi

– Dattijon Arewa Farfesa Ango Abdullahi yace bai ki a raba kasar nan ba

– Farfesan yace idan ya zama dole a raba Kasar Najeriya to sai a rabu

– Dattijon yace Yankin Arewa sun dade su na hakuri a Najeriya

Farfesa Ango Abdullahi yace idan ya zama dole kowa ya balle a kasar ai sai ayi. Dattijon yace Arewa ba ci-ma-zaune ba ce kuma ba ta taba zama ba kuma ba za ta zama ba. Ango yace ba yau aka saba raba kasa a Duniya ba kuma an zauna lafiya.

Ango Abdullahi

Na fada na kara fada Arewa ba matsiyaciya ba-Ango Abdullahi

NAIJ.com ta samu wani rahoton hira da aka yi da Dattijon Arewa Farfesa Ango Abdullahi inda yace babu wanda ya isa yayi wa Yankin Arewa gori don kuwa ita ta gina kasar nan. Farfesan yace yana kan bakan sa na raba kasar.

KU KARANTA: Mutanen Adamawa sun shiga uwar-bari

Inyamurai: Mun yi hakuri haka ko matar kace ta nemi saki ai sai ku rabu-Ango Abdullahi

Gwamnati za ta dauki mataki game da kiran korar Inyamurai daga Arewa

A tattaunawar Ango Abdullahi yace ‘Yan Arewa sun yi hakuri da Inyamuran kasar haka nan wanda ko matar kace ta nemi saki ai sai ku rabu idan har auren ya ki dadi. Farfesan ya kara da cewa su manyan kasar ne su ka hana ruwa gudu.

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa ba za ta bari wani abu na rikici ya faru ba a fadin kasar. Kwanakin baya wani Dattijon Arewa Dr. Junaidu Muhammad ya koka da yadda Gwamnatin Tarayyar tayi tsit ba ta dauki wani mataki ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

El-Rufai ya sa a kama wadanda su kayi wa Inyamurai barazana

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56

Gwamnatin tarayya ta share ma Zamfara awaye da biliyan 56
NAIJ.com
Mailfire view pixel