Wani Gwamna ya kori Ma’aikata ya nada ‘Yar uwar sa

Wani Gwamna ya kori Ma’aikata ya nada ‘Yar uwar sa

– Gwamnan Jihar Imo ya nada ‘Yar uwar sa cikin Gwamnatin Jihar

– Rochas Okorocha ya salami Ma’aikata da dama kwanaki

– Mun samu labari cewa an nada sababbi a halin yanzu

Kwanaki Gwamna Okorocha yayi zazzaga

An maido kadan daga wanda aka sallama

Sai dai kuma wannan karo an yi ‘yar gida

Wani Gwamna ya kori Ma’aikata ya nada ‘Yar uwar sa

Gwamna ya Rochas ya nada 'Yar uwar sa a Gwamnati

Gwamnan Jihar Imo Rochas Owelle Okorocha yayi zazzagar gaske kwanaki inda ya sallami Kwamishinoni da sauran masu rike da mukamai. Yanzu dai an fara nada wasu kuma ciki har da wata ‘Yar uwar sa Ogechi Ololo.

KU KARANTA: Azumi: Mabiya Kwankwaso sun ji ruwan alheri

Wani Gwamna ya kori Ma’aikata ya nada ‘Yar uwar sa

Matar Mai Girma Gwamnan Jihar Imo

Gwamna Rochas ya nada Misis Ololo a matsayin Mataimakiyar Shugaban Ma’aikatan cikin gidan Gwamna. Mai girma Okorocha yace ba da wani bata lokaci ba kuma za su shiga ofis domin su dukafa da aiki.

A can kwanakin baya Gwamnan Jihar na Imo yace Mai dakin sa, Nkechi Okorocha ta rike ma’aikatu har hudu na Jihar a baya a Gwamnatin sa. Hakan ta sa aka jinjinawa Matar Gwamnan aka ba ta kyautar lambar yabo. Wasu dai na ganin ya maida gidan Gwamnatin kamar na gado.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hatsaniya game da maganar korar Inyamurai daga Arewa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel