Tattalin arziki: Biliyan talatin mutan Najeriya suka kashe a Umarar bana

Tattalin arziki: Biliyan talatin mutan Najeriya suka kashe a Umarar bana

- Kiyasin masana ya gano yada kudaden Najeriya ke sulalewa kasashen waje

- Biliyoyin kudade addinai daban daban ke amshewa mutane da alkawarin biyansu a wata rayuwa bayan sun mutu

- Mutanen Najeriya sun fi na ko'ina son zuwa yawon ibada gabas ta tsakiya

Hangen nesa irin na masu bin kwakwaf na yadda ake kashe kudaden Najeriya a kasashen waje don bude ido ko neman lada ya saka hamshakin dan jarida kuma mai nazari kan sabgogin gwamnati da jama'a, Malam Jaafar Jaafar na Kanawa, wallafa yadda musulmai suka aike da kudadensu kasar Saudiyya don ibada da neman lada.

A shafinsa na dandalin sada zumunta na Facebook dai, mawallafin, yayi kiyasin kudaden da jama'ar Najeriya suka kashe a bana, inda yace kudin sun kai adadin biliyan ishirin da takwas, (N28b).

KU KARANTA KUMA: Inyamurai: Mun yi hakuri haka ko matar kace ta nemi saki ai sai ku rabu-Ango Abdullahi

Tattalin arziki: Biliyan talatin mutan Najeriya suka kashe a Umarar bana
Tattalin arziki: Biliyan talatin mutan Najeriya suka kashe a Umarar bana

"A bana dai kusan mutum dubu arba'in (40,000) ne dai suka kwashi jiki zuwa umara a kasar Saudiyya, kowannensu kuwa zai kashe akalla dubu dari bakwai kan kudin jrigi, biza, otal, da abinci sannan guzuri, da zirga-zirga a can Saudiyyar, idan ka ninka kudin zuwa yawan maziyartan, zaka sami jimillar kusan biliyan talatin, a haka kuma tuna fa, wasu zasu kashe fin haka da ninki biyu ko uku.," ya wallafa.

Wannan rubutu nasa ya tada kura da yamutsa hazo, inda wasu ke kushewa da tir, wasu kuwa suna kare ra'ayin dan jaridar kan gaskiyar kiyasin nasa, duk da dai bayyi bayanin ko yana goyon bayan kashe makudan kudaden a kasar waje ba ko a'a .

Shi dai malam Jaafar Jaafar, ya saba tsokaci kan batu da kan jawo cece-kuce tsakanin al'umma, musamman kab batun al'adu, adalcin gwamnati, cin hanci da rashawa, harma da addini ko al'ada. Da yawa daga masu bibiyar shafinsa sukan zarge shi da yin zagon kasa ga siyasarsu da ma addini. Shi dai Malamin, bai fiye tanka musu ba ko cewa ko ga bangaren da ya dosa ba.

Ana iya samun labarun jaridarsa ta Daily Nigerian ko a shafinsu na yanar gizo, ko ta shafinsa a dandalin sada zumunta na Facebook.

Batun kashe kudaden kasa a kasashen waje kuwa, sai ku biyo mu ku tafka muhawara ko hakan asarar kudi ce tunda ana zazzafar yunwa a wasu jihohin kuma talauci ya karu tsakanin al'umma, ku tattauna wanne ya fi, mikawa Saudiyya kudin mu, ko kuwa taimakawa a habaka arzikin jama'a a gida?

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel