Kowa ya je yayi katin zama dan Kaduna – Inji El-Rufai

Kowa ya je yayi katin zama dan Kaduna – Inji El-Rufai

- Gwamnatin El-Rufai ta Kaduna ta sanar da fara yin rijistar ga mazauna jihar

- Kwamishinan Kasafin kudin Jihar, Mohammed Abdullahi ne ya sanar da haka

- Gwamnatin ta fitar da haka ne saboda ta san iya adadin mutanen da ke zama a karkashinta sannan kuma ta iya wadata al’umman da ababen more rayuwa

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da fara yin rijistar ga duk wani mazaunin jihar domin sanin iya adadin mutanen dake zama a cikinta.

Kwamishinan Kasafin kudin Jihar, Mohammed Abdullahi ne ya sanar da haka ranar Laraba da ya ke nasa rijistan a Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Abin kunya: Saudi ta aikowa Najeriya dabino sadaka amma an saida

Kowa ya je yayi katin zama dan Kaduna – Inji El-Rufai

Kowa ya je yayi katin zama dan Kaduna, Inji El-Rufai

Mohammed ya ce gwamnati ta fitar da haka ne saboda ta san iya adadin mutanen da ke zama a karkashinta sannan kuma ta iya wadata al’umman da ababen more rayuwa.

Gwamnati ta umurci duk wani wanda zai zauna a jihar da zai kai kwanaki 180 da ya tabbata yayi wannan rijista.

Ya ce: “wasu daga cikin dalilan yin wannan rijista shine domin gwamnati ta iya samarwa mutane ababen more rayuwa da kuma kara samar da tsaro a jihar.”

Ya kara da cewa gwamnati na shirin samar wa mutanen jihar ababen more rayuwa wanda sai mutum yana da wannan shaida ne za iya amfana da wasu da ga cikin su.

Ya ce mutane su ziyarci wuraren da gwamnati ta kirkiro domin yin rijistan ko kuma a je ma’aikatar samarda da katin shaidan zama dan kasa domin a yi rijista.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel