Zinedine Zidane zai zama Kocin Kasar Faransa

Zinedine Zidane zai zama Kocin Kasar Faransa

– Kocin Kungiyar Real Madrid zai horar da Faransa wata rana

– Shugaban Kungiyar kwallon kafan kasar ya fadi haka

– Kocin na Real Madrid ya bugawa Kasar Faransa kwallo

Noel Le Graet yace Koci Zidane zai horar da Kasar Faransa wata rana. A cewar sa hakan zai yi kyau ganin Kocin tsohon Dan wasan kasar ne. Zidane ya lashe kofuna da yana wasa da kuma yanzu da yake horaswa.

Zinedine Zidane zai zama Kocin Kasar Faransa

Zinedine Zidane dauke da kofin UEFA Champions League

Shugaban Kungiyar kwallon kafan kasar Faransa Noel Le Graet yace wata rana Koci Zinedine Zidane na Real Madrid zai horar da Kasar Faransa don kuwa hakan zai yi daidai ganin yadda tsohon Dan wasan ya taso.

KU KARANTA: Babban 'Dan wasan Real Madrid ya haihu

Zinedine Zidane

Zidane a wasan sa na karshe da Kasar Faransa

Kocin na Real Madrid ya bugawa Kasar Faransa wasa inda har ya ci kofin Duniya ya kuma kai gaf da cin wani a karshen rayuwar sa. Shugaban FFF na kwallon kafar kasar Faransa yace yayi mamakin yadda Zidane din ya gawurta zuwa yanzu.

Real Madrid ta lashe gashe gasar La-liga karo na farko cikin shekaru wajen 5 karkashin Koci Zinedine Zidane daga nan Kungiyar ta lashe Gasar UEFA Champions League na zakarun Nahiyar Turai.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An yaye wasu Sojojin saman Najeriya har su l0

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel