Gwamnati za ta dauki mataki game da kiran korar Inyamurai daga Arewa

Gwamnati za ta dauki mataki game da kiran korar Inyamurai daga Arewa

– Mukaddashin Shugaban Kasa Osinbajo yace babu maganar raba kasa

– Osinbajo ya gana da Shugabannin Yankunan kasar kwanan na

– Wasu Jama’a na kira kowa ya zauna a kasar sa

Gwamnati ta dauki matakin kare duk wani rikici a Najeriya

Wasu na kira a raba kasar wasu kuma na kira a salami Inyamurai

Osinbajo ya gana da manyan kasar cikin ‘yan kwanakin nan

Osinbajo

Babu dalilin tada hankali Inji Osinbajo

Ministan yada labarai Lai Mohammed ya bayyana cewa dama dai Gwamnatin Tarayya za ta dauki mataki game da masu kiran a raba kasar ko kuma Inyamurai su bar yankin Arewa. Tuni kuwa Farfesa Osinbajo ya fara ganawa da Shugabannin Arewan da na Kudu.

KU KARANTA: Ba mu shirya yaki ba Inji Gwamnan Jihar Imo

Gwamnati za ta dauki mataki game da kiran korar Inyamurai daga Arewa

Osinbajo ya gana da wasu Shugabannin Arewa

A shekaran jiya Osinbajo ya zauna da Dattawa da manyan Arewa yayin da kuma jiya ya zauna da Shugabannin kasar Ibo kashegarin ranar. Yau ne kuma zai zauna da dukkan su baki daya domin hana aukuwar wani rikici inda yace babu dalilin ta da hankali a kasar.

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa ba za ta bari wani abu ya faru ba a fadin kasar. Kwanakin baya wani Dattijon Arewa Dr. Junaidu Muhammad ya koka da yadda Gwamnatin Tarayyar tayi tsit ba ta dauki wani mataki ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani tsohon Soja ya gargadi masu shirin raba kasa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel