Dukiyoyi sun salwanta a sabuwar rikicin ƙabilanci data ɓarke a Benuwe

Dukiyoyi sun salwanta a sabuwar rikicin ƙabilanci data ɓarke a Benuwe

- Jama’an kabilun Tiv da Jukun sun sake baiwa hammata iska a ranar Laraba

- Wannan rikici dai ya sake barkewa ne a daidai gaban barikin soja

Jama’an kabilun Tiv da Jukun sun sake baiwa hammata iska a ranar Laraba 14 ga watan Yuni, wanda hakan yayi sanadiyyar kona gidaje da dama tare da bacewar wasu mutane daga bangarorin biyu.

Wannan rikici dai ya sake barkewa ne a daidai gaban barikin rundunar mayakan sojin sama dake garin Makurdi, mazauna garin sun shaida ma jaridar daily Trust cewar maharan sun kona sama da gidaje 20, ciki har da gidan sarkin Kyurav, Uir Udi.

KU KARANTA: Watan Ramadana: Kwankwaso yayi rabon shinkafa

Sai dai sarkin karamar hukumar Makurdi, Sule Abenga ya shaida ma majiyar NAIJ.com cewar matasan yankin ne suka kawo masa rahoto game da harin da aka kai musu.

Dukiyoyi sun salwanta a sabuwar rikicin ƙabilanci data ɓarke a Benuwe

daya daga cikin Gidan da aka kona

“Matasan sun bayyana min an kona gidaje dayawa har da na sarkinsu, sa’annan sun ce wasu daga cikin yan uwansu sun bace, amma dai ban tabbatar da wannan ba, daga nan sai na basu hakuri, kuma na wuce fadar Sarkin Tiv a garin Gboko na shaida masa.”

Shima Kaakakin yansandan jihar, Moses Joel Yamu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace sun kama mutane hudu dake da hannu cikin kai harin.

Wannan rikici dai ya samo asali ne tun a ranar 22 ga watan Mayu, a lokacin da wasu samari su biyu yan kabilar Jukun da Tiv suka samu sabani a dandalin shaye shaye, daga nan ne fa suka fara fada da juna, har abin ya zama fadan kabilanci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani mutumi a yace Buhari ya mutu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Duba da sakamakon babban zaben PDP, anya Atiku bai yi kamun gafiyar baidu ba?

Atiku ya saki reshe ya kama ganye a sanadiyyar sauyin shuwagabanni da PDP ta yi
NAIJ.com
Mailfire view pixel