Ruwa ya karya gadoji a Adamawa, kalli yadda jama’a ke tsallaka rafi

Ruwa ya karya gadoji a Adamawa, kalli yadda jama’a ke tsallaka rafi

- Ruwan sama ya karya gada data tilo dake kauyen Bazza

- Gadojin sun karye ne sakamakon ruwan saman da aka kwashe awanni ana zabgawa

Wani ruwa da aka maka a jihar Adamawa kamar da bakin kwarya ya karya gada data tilo dake kauyen Bazza data hade jihar Adamawa da jihar Borno, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Wakiliyar al’ummar Adamawa ta Arewa, Sanata Binta Garba tace gadojin sun karye ne sakamakon ruwan saman da aka kwashe awanni ana zabgawa, sa’adda kasuwar garin dake ci mako mako ke cike da jama’a

KU KARANTA: Dakarun Soji sun kakkaɓe ɓarayin shanu daga dajin jihar Kaduna

Sai dai, tun a baya, dama Sojoji suka fara tarwatsa wannan gadoji da nufin dakatar da yan Boko haram daga shigowa jihar Adamawa, sakamakon sun hada iyakar garuruwan Gwoza da Askira Uba na jihar Borno da kuma Michika a Adamawa.

Ruwa ya karya gadoji a Adamawa, kalli yadda jama’a ke tsallaka rafi

Yadda jama’a ke tsallaka rafi

Sanata Binta tace duk da sanya gyaran gadan a cikin kasafin kudi a shekarun baya, amma gwamnati tayi shakulatin bangaro da aikin gayaran gadar, har mai aukuwa ta auku.

Ruwa ya karya gadoji a Adamawa, kalli yadda jama’a ke tsallaka rafi

Gadar data karye

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hira da Sojan Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel